Ibrahim Garba
Ibrahim Garba | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Kaduna, 25 ga Faburairu, 1957 (67 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Malami, geologist (en) , academic administrator (en) da ilmantarwa | ||
Kyaututtuka |
gani
| ||
Mamba | Makarantar Kimiyya ta Najeriya |
Ibrahim Garbasauti (Taimako·bayani) masanin ilimin kasa ne kuma mai kula da jami'a a Najeriya. Shi ne tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sai Kabir Bala ya gaje shi. Ya kuma taba zama shugaban Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil[1][2]. Garba dan asalin Riruwai ne a jihar Kano.
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Garba ya yi digiri na farko da na biyu a fannin Geology duk a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma Phd a Kwalejin Imperial da ke London.[3]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Garba ya yi aiki a ma'aikatar ma'adinai da karafa ta tarayya Abuja a matsayin Darakta-Janar na Ofishin Cadastre na Ma'adinai na Najeriya. Ya jagoranci ci gaba da aiwatar da Tsarin Ma'adinai Cadastre a Najeriya.
Rigimar zamba
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 29 ga Maris, 2023, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da Ibrahim Garba gaban kotu kan badakalar Naira biliyan 1. An tuhume shi da laifin karkatar da kudaden da aka tanada a otal din taro na Kongo, Zaria tsakanin 2013 zuwa 2016.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Garba takes charge at ABU". The News Nigeria. Retrieved September 13, 2015.
- ↑ "Council appoints Professor Ibrahim Garba as ABU new Vice". Daily Post. Retrieved September 13, 2015.
- ↑ "Prof Ibrahim Garba: The 14th Vice-Chancellor Of ABU Zaria | The Abusites" (in Turanci). 2021-05-25. Retrieved 2023-10-19.
- ↑ Times, Premium (2023-03-29). "EFCC arraigns former vice-chancellor, bursar for N1 billion fraud". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-03-29.