Jump to content

Ike Ekweremadu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ike Ekweremadu
Deputy President of the Nigerian Senate (en) Fassara

5 ga Yuni, 2007 - 9 ga Yuni, 2019
Ibrahim Mantu - Ovie Omo-Agege
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - ga Yuni, 2007
Ben-Collins Ndu
District: Enugu West
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya


District: Enugu West
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya


District: Enugu West
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya


District: Enugu West
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya


District: Enugu West
Rayuwa
Cikakken suna Ike Ekweremadu
Haihuwa Jihar Enugu, 12 Mayu 1962 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
Jami'ar Abuja
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Ike Ekweremadu (an haife shi 12 ga watan mayun, 1962) a kauyen Amachara Mpu da ke Karamar hukuma Aninri a Jihar Enugu.[1] Ɗan Nijeriya ne, ɗan siyasa kuma lauya, wanda ya kasance sanata a majalisar dattawan Nijeriya tun daga watan Mayu shekara ta 2003. Dan jam'iyar People's Democratic Party (PDP) ne, kuma shine Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa karo na uku (6th, 7th and 8th) kenan.[2][3] A ranar 23 ga Yuni 2022, an tuhumi Ekweremadu tare da matarsa a Kotun Majistare ta Burtaniya da laifin haɗa baki don shirya Safarar ɗan shekara 21 zuwa Burtaniya domin cire wani sassa a jikin sa.[4] An same shi da laifi a ranar 23 ga watan Maris 2023 a Kotun hukunta manyan laifuka ta, Old Bailey.[5]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ike Ekweremadu a Amachara Mpu da ke karamar hukumar Aninri ta jihar Enugu, kuma dan ƙabilar Igbo ne. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a fannin shari'a a Jami'ar Najeriya, sannan aka kira shi zuwa Nigerian Bar a 1987. Ya kuma yi digirin digirgir a fannin shari'a a Jami'ar Abuja, Najeriya.[6][7][8]

Naɗi[gyara sashe | gyara masomin]

Naɗin Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa shi a matsayin shugaban zartarwa na karamar hukumar Aninri a ƙarƙashin jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) a shekarar 1997 kuma ya lashe mafi kyawun shugaban majalisar na shekara, a 1997.[6][9]

ECOWAS[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin watan Satumba na 2009, an naɗa shi shugabancin kwamitin rikon kwarya na ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) don yin aikin dawo da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar.[10] An zaɓe shi mataimakin shugaban majalisar ECOWAS na farko kuma ya zama shugaban majalisar yankin a watan Agustan 2011.[11]

Fagen Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

The Guardian and erstwhile Federal Commissioner of the Nigerian National Human Rights Commission [NHRC] Comrade Emmanuel Onwubiko advocacy visit to the Deputy Senate President Senator Ike Ekweremadu

A ranar 12 ga Afrilu 2003 aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dattawan Najeriya.[12] A watan Satumban 2003, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yaɗa labarai, Cif Ekweremadu ya bayyana cewa majalisar za ta yi bincike mai zurfi kan zargin karɓar cin hanci da ministan babban birnin tarayya (FCT) Mallam Nasir el-Rufai ya yi.[13] Dangantaka tsakanin Nasir El-Rufai da majalisar dattawa ta ci gaba da yin tsami, kuma daga karshe an tuhumi El-Rufai da laifin almundahana a shekarar 2008.[14][15] A shekarar 2005, Sanata Kenechukwu Nnamani ya doke Ike Ekweremadu a takarar shugaban majalisar dattawan Najeriya.[16]

Zargi[gyara sashe | gyara masomin]

An kama waɗanda ake zargi[gyara sashe | gyara masomin]

An kama tsohon Sanatan da matarsa Beatrice a ƙasar Birtaniya kan laifin kai wani yaro ƙasar don cire wani sashen jikinsa.[17][18][19][20][21][22][23] Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu bayan gudanar da bincike. Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da binciken ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.[24]

Zaman kotu akan shari'ar zargin satar Yaro[gyara sashe | gyara masomin]

▶Bayan zaman kotun na farko kotun ta hana belin shi Ekweremadu da matarsa, hakan na nufi zasu cigaba da kasancewa a tsare har sai sun sake gurfana gaban kuliya a ranar 7 ga watan Yulin 2022 mai zuwa.[25]

▶Ranar 5 ga watan Agusta, An ɗage shari'ar da'ake ma Sanata Ekweremadu zuwa watan 31 ga watan Oktoba, amma sauraron ƙara da gabatar da shaidu a shari'ar sai watan Mayu na shekarar 2023 Oktoba.[26]

Kotu ta kama shi da laifi[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 23 ga watan Maris 2023 Ekweremadu, da matarsa da Dokta Obinna Obeta an same su da laifin haɗa baki wajen yin amfani da kodar mutumin. Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun Old Bailey cewa an kawo wanda aka kashen zuwa Burtaniya a shekarar 2022 don cire kodar a cikin wani ɗaki na sirri, akan fam 80,000, a asibitin Royal Free Hospital, London. Masu gabatar da ƙara sun tabbatar da mafi ƙaranci zaman gidan yari, akan shari'ar safarar sata sassan bil'adama shi ne, hukuncin ɗaurin rai-da-rai ne.[27] Za a cire gabobin a ba wa ‘yar ma’auratan – ɗiyar ma'auratan an wanke ta daga wannan tuhume-tuhume.[28]

Zargin rashawa[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yulin 2018, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kasar najeria ta gayyaci shi don amsa tambayoyi kan zargin rashawa.

Ce-ce kuce[gyara sashe | gyara masomin]

An kai masa hari[gyara sashe | gyara masomin]

Ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2019, an Ike Ekweremadu ya ziyarci Nuremberg, ƙasar Jamus don halartan wani taro da suka shirya, wasu fusatattun matasa suka far masa. Jim kaɗan da faruwar hakan sai bidiyo ya bayyana soshiyal midiya inda aka ga Ekweremadu yana kokarin neman tsira da rayuwarsa a yayin harin.[29]

Sukar Peter Obi. A wani bidiyon kuma da ya bayyana shima a soshiyal midiya, anji Ekweremadu na faɗar wani yani a nigeria ba za su yarda su mara ma Peter Obi baya ba a babban zaben shugaban kasa.

Kyaututtuka da karramawa[gyara sashe | gyara masomin]

 • CFR, Knight of the Good Shepherd, Ikeoha Ndigbo.[30]
 • Fitaccen ɗan ƙasar Rotary Club na Duniya 2017.[31]
 • Dr. Kwame Nkurumah Kyautar Jagorancin Afirka (2005).[32]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. http://biography.hi7.co/biography-of-ike-ekweremadu--senator--lawyer--politician--enugu-state-celebrity-56651dde59b03.html
 2. Fashagba, Joseph Yinka; Ajayi, Ola-Rotimi Matthew; Nwankwor, Chiedo, eds. (2019). "The Nigerian National Assembly". Advances in African Economic, Social and Political Development (in Turanci). doi:10.1007/978-3-030-11905-8. ISBN 978-3-030-11904-1. ISSN 2198-7262. S2CID 211384008.
 3. Khadijat Lawal (23 June 2022). "Things you should know about Ekweremadu, lawmaker and lawyer arrested for organ harvesting". Daily Trust. Retrieved 28 June 2022.
 4. "Two people charged with conspiracy offences linked to allegations of organ harvesting". Metropolitan Police. Archived from the original on 27 June 2022. Retrieved 23 June 2022.
 5. "Organ-trafficking plot Nigerian politician and wife guilty". BBC.
 6. 6.0 6.1 Ogbonnia, Chiedozie Alex (May 18, 2013). "Ekweremadu at 51 – a profile in grace". Vanguard Newspaper. Retrieved August 31, 2021.
 7. Tony Adibe (16 May 2022). "After 20 years in Senate, Ekweremadu eyes Enugu Govt House". Daily Trust. Retrieved 28 June 2022.
 8. This Day (2017). "Ekweremadu: A Stabilising Force in Senate". This Day.
 9. Cyril (10 May 2022). "Ekweremdu @ 60: bringing Robust Experience on the table". The Sun. Unknown parameter |access- date= ignored (help)
 10. "Ekweremadu Heads Ecowas Committee In Country". Daily Trust. September 11, 2009. Retrieved 2009-09-13.
 11. "Ekweremadu at ECOWAS". 17 August 2011.
 12. "Shady Deals". Newswatch Communications Limited. 8 June 2003. Archived from the original on 25 April 2006. Retrieved 2009-09-14.
 13. "Senate Resolves to Probe FCT Minister's Bribery Allegation". Vanguard (Nigeria). 18 September 2003. Retrieved 2009-09-13.
 14. "Profile: Mallam Nasir el-Rufai". BBC News. 7 September 2004. Retrieved 2009-09-13.
 15. "Nigeria ex-minister is wanted man". BBC News. 22 December 2008. Retrieved 2009-09-13.
 16. "Nnamani Emerges Senate President". This Day Online. April 5, 2005. Archived from the original on 2005-04-26. Retrieved 2009-09-13.
 17. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-06-27. Retrieved 2022-08-04.
 18. "UK court denies Ekweremadu, wife bail over child trafficking, organ harvesting". The Guardian Nigeria. Retrieved 23 June 2022.
 19. "UK Police Arrest Ike Ekweremadu, Wife For Organ Harvesting". Channels Television. Retrieved 24 June 2022.
 20. "Alleged organ trafficking: Ekweremadu, wife risk long jail term if convicted". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-06-24. Retrieved 2022-06-24.
 21. "Ekweremadu: International passport of organ donor reveals he's 21". Vanguard News (in Turanci). 2022-06-24. Retrieved 2022-06-24.
 22. "Ekweremadu, Wife Denied Bail by UK Magistrate's Court". YouTube. Arise News. Retrieved 25 June 2022.
 23. "Nigerian couple charged with plotting to get child to UK to harvest organs". Reuters. Retrieved 25 June 2022.
 24. https://hausa.legit.ng/news/1476135-zunuban-ike-ekweremadu-manyan-rigingimu-4-da-tsohon-mataimakin-shugaban-majalisar-dattawan-ya-fada-ciki/
 25. https://www.voahausa.com/a/kotu-ta-hana-belin-tsohon-mataimakin-shugaban-majalisar-dattawan-najeriya-ekweremadu-da-matarsa-a-landan/6631155.html
 26. https://www.bbc.com/hausa/articles/c51d3n442jzo
 27. . BBC News. 23 March 2022 plot Nigerian politician and wife guilty https://www.bbc.co.uk/news/uk-england-london-65013545title=Organ-trafficking plot Nigerian politician and wife guilty Check |url= value (help). Retrieved 23 March 2022. Missing or empty |title= (help)
 28. . BBC News. 23 March 2022 plot Nigerian politician and wife guilty https://www.bbc.co.uk/news/uk-england-london-65013545title=Organ-trafficking plot Nigerian politician and wife guilty Check |url= value (help). Retrieved 23 March 2022. Missing or empty |title= (help)
 29. https://hausa.legit.ng/news/1476135-zunuban-ike-ekweremadu-manyan-rigingimu-4-da-tsohon-mataimakin-shugaban-majalisar-dattawan-ya-fada-ciki/
 30. "Home".
 31. Dennis Agbo (29 November 2017). "Ekweremadu bags World's Outstanding citizen award". Vanguard.
 32. Sufuyan Ojeifo (12 May 2014). "Ekweremadu: Praxis of persistent, consistent loyalty". Vanguard.