Itunu Hotonu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Itunu Hotonu
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 18 ga Janairu, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Tsaron Nijeriya
Jami'ar Najeriya, Nsukka
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a naval officer (en) Fassara da Masanin gine-gine da zane
Digiri admiral (en) Fassara

Rear Admiral Itunu Hotonu (an haife ta a ranar 18 ga watan Janairu shekarar 1959) hafshiyar sojan ruwa ce na kasar Najeriya . Daya daga cikin shugabannin mata na farko kuma daga cikin wadanda suka fara zama masu zanen gine-gine (Architect) a cikin rundunar sojojin ruwa ta Najeriyar, ta taba aiki a matsayin mai koyar da malama a kwaleji da kuma kasashen waje kamar a kasar Laberiya . A watan Disamba na shekarar 2012 ta zama mace ta farko a Afirka.[1] [2][3][4][5]

Farkon rayuwa da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Itunu Hotonu an haife ta ne da suna (amatsayin Itunu Tomori) ranar 18 ga watan Janairu shekarar 1959[6]. Bayan ta kai shekara 13 sai ta yanke hukuncin cewa ta so ta zama injiniyar gine-gine.[7] Hotonu ta karanci fannin gine-gine a Jami'ar Najeriya, inda a kullun ita ce mace kaɗai a cikin karatun.[8] Bayan da ta sauke karatu sai ta yi aiki a ofishin injiniyar gine-gine har na tsawon shekaru biyu yayin da ta yi karatun digiri na uku.

Hotonu ta nemi shiga cikin Injiniyoyi na Rundunar Sojojin Najeriya amma ance mata babu mukamai ga mata a wannan fannin.[9] Sannan ta nemi izinin Navy, wanda bashi da hani game da jinsi. An karbe ta a matsayin mai Neman zama jami'a a Kwalejin Tsaro ta kasa, Abuja, a cikin 1985.[10] Ita ce mace ta farko da ta halarci makarantar kuma ta kammala a matsayin ta na gaba daya wacce take aji na 73. Ta lashe lambar yabo ta kwamandan-sarki da kuma lambar yabo ta kwamandan domin kyakkyawan aikin bincike. Hotonu ta zama daya daga cikin na farko da ya fara aiki a rundunar sojojin ruwan Najeriya.

Hotonu ita ce mace ta farko da ta fara aiki a matsayin malama mai Umurni (instructor) Armed Forces Command and Staff College a Jaji .[11] [12] A shekarar 2012 ta kwashe lokaci a Laberiya wajen horar da mata a cikin sojojin kasar. An haife ta zuwa matsayin girmamawa ta baya a watan Disamba shekarar 2012, ta zama mace ta farko a Afirka.[13][14]

Rayuwar mutum[gyara sashe | gyara masomin]

Hotonu ta auri mai zane (Architect) Abayomi Hotonu wanda a tare dashi tana da yara uku.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Ambode's wife, others laud 50 years of women's contributions to Lagos". Daily Times Nigeria (in Turanci). 2017-05-19. Retrieved 2020-05-03.
  2. Editor, Online. "Lagos @ 50: Making heroine of the girl-child New Telegraph Online New Telegraph". New Telegraph (in Turanci). Retrieved 2020-05-03.CS1 maint: extra text: authors list (link)[permanent dead link]
  3. "THE ROLE OF WOMEN AND GIRLS IN PEACE INITIATIVES IN NIGERIA" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2018-02-19. line feed character in |title= at position 31 (help)
  4. Published. "NIA advised to train, mentor aspiring female architects". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2020-05-03.
  5. Nkasiobi, Oluikpe. "Female Architects Seek Role In Decision-Making Process, Leadership". Independent News.
  6. "FIRST WOMEN: First Nigerian Woman To Become A Rear Admiral In the Nigerian Navy". Woman Nigeria. 21 September 2016. Archived from the original on 11 March 2019. Retrieved 30 November 2017.
  7. "Itunu Hotonu: Africa's First Female Admiral's Journey To The Top". Answers Africa. 21 December 2016. Retrieved 30 November 2017.
  8. "Women who want to break boundaries must be ethical —Rear Admiral Itunu Hotonu » Features » Tribune Online". Tribune Online (in Turanci). 2016-12-25. Retrieved 2020-05-03.
  9. editor (2019-09-13). "Aisha Buhari Calls for Eradication of Gender Bias in Military". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2020-05-03.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  10. "'If I die, I DIE!'". The Nation Nigeria. 6 May 2017. Retrieved 29 November 2017.
  11. "How to achieve gender balance — Hotonu - P.M. News". www.pmnewsnigeria.com. Retrieved 2020-05-03.
  12. Published. "Hotonu advises women on leadership". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2020-05-03.
  13. "Most Senior Female Military Officer Speaks On Gender Issues In Military". Channels Television. Retrieved 2020-05-03.
  14. "Adenike Osofisan Deserves National Honour – UI VC -". The NEWS. 2019-06-10. Retrieved 2020-05-03.