Jimmy Wales
Jimmy Donal Wales (/ˈdʒɪmi ˈdoʊnəl weɪlz/); (An haife shi ranar 7 ga watan Augustan shekara ta 1966) a garin Huntsville da ke jihar Alabama a Ƙasar Amurka, yana zaune a Landon da ke Ƙasar Ingila. ɗan kasuwan Kasar Tarayyar Amurka ne.[1][2] Jimmy Wales da Larry Sanger ne suka ƙirƙiri babbar manhajar Wikipidiya a shekara ta 2001. Ya yi karatu a Jami'ar Auburn da Jami'ar Jihar Alabama, Tuscaloosa inda ya samu shaidar digiri na biyu a Jami'ar jihar Indiana, shahararren dan kasuwan yanar gizo ne, kuma yana da adadin kuɗi sama da dala miliyan daya ($1,000,000) a shekara ta dubu biyu da sha hudu (2014).
Farkon rayuwa da karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Wales a Huntsville, Alabama, da tsakar dare a ranar 7 ga watan Augustan, shekara ta 1966, amma shaidar haihuwarsa tana nuna 8 ga watan Augutane.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Shugabanci
[gyara sashe | gyara masomin]Shi ne shugaban Wikia, Inc. tun daga shekara ta 2004 har zuwa yau, Mazaunin Shugaban Wikimedia Foundation daga shekara ta 2003–2006, Chair emeritus of Wikimedia Foundation daga shekara ta 2006 har zuwa yanzu, shi ya amshi Florence Devouard a matsayin shugaban Wikimedia Foundation, Babban Dan kungiyar wikimedia Foundation Creative Commons ne, kuma yana daga cikin masu bada shawara a Sunlight Foundation da MIT Center for Collective Intelligence, a Guardian Media Group ya daina bada shawara a watan Afrilun shekaran 2017.
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Matansa sune;
- Pamela Green daga shekara ta (1986 zuwa 1993),
- Christine Rohan (1997–2011), sai
- Kate Garvey. Wanda tun daga shekara ta 2012 har yanzu suna tare. 'Ya'yansa guda 3 ne mata.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Jimmy Wales [@jimmy_wales] (September 16, 2019). Jimmy Wales [@jimmy_wales] (September 16, 2019). "I just became a UK citizen, quite happy about that. It occurs to me that perhaps a few MPs should actually take the "Life in the UK" test and study the manual!" (Tweet) – via Twitter.
- ↑ Horovitz, David (January 7, 2011). "Jimmy Wales's benevolent Wikipedia wisdom". The Jerusalem Post. Archived from the original on August 3, 2018. Retrieved December 26, 2017.
- Wikipedia articles with DBLP identifiers
- Wikipedia articles with GND identifiers
- Wikipedia articles with ISNI identifiers
- Wikipedia articles with LCCN identifiers
- Wikipedia articles with NKC identifiers
- Pages with red-linked authority control categories
- Wikipedia articles with NLI identifiers
- Wikipedia articles with faulty NLP identifiers
- Wikipedia articles with PLWABN identifiers
- Wikipedia articles with SUDOC identifiers
- Wikipedia articles with Semantic Scholar author identifiers
- Wikipedia articles with VIAF identifiers
- Wikipedia articles with WorldCat-VIAF identifiers
- 'Yan kasuwan Tarayyar Amurka
- Ma'aikatan Wikipedia