Jump to content

Joseph Folaha Odunjo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Joseph Folaha Odunjo
Rayuwa
Haihuwa Abeokuta, 1904
Mutuwa 1980
Karatu
Makaranta UCL Institute of Education (en) Fassara
Harsuna Yarbanci
Sana'a
Sana'a Marubiyar yara

Cif Joseph Folaha Odunjo (ya rayu daga shekarar 1904– zuwa shekarar 1980). Marubuci ne, malami kuma ɗan siyasa ɗan ƙasar Najeriya wanda aka fi sani da ayyukansa na adabin Yarabawa.[1][2][3][4][5]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Odunjo a Ibara, Abeokuta a shekarar 1904.[6] Ya yi karatu a St Augustine's Primary School, Abeokuta, Catholic Higher Elementary Training School da London Institute of Education.

Aikin koyarwa da Rubutu

[gyara sashe | gyara masomin]

Odunjo ya fara aikin koyarwa ne a matsayin shugaban makaranta na Kwalejin horar da Katolika da ke Ibadan daga shekarun 1924 zuwa 1927 sannan ya zama shugaban almajiransa na St Augustine, Abeokuta. A matsayinsa na malami, ya kafa kungiyar malaman Katolika ta tarayya don tattaunawa da mishan na Katolika a madadin malaman mishan. Odunjo ya kasance malami kuma shugaban makarantun Katolika daban-daban tun daga shekarun 1940 zuwa 1950.[7] Ayyukan da ya wallafa a shekarar 1958 na ɗaya daga cikin rubuce-rubucen farko na harshen. Ya rubuta litattafai da yawa, wasan kwaikwayo, kasidu da rubutu a cikin harshen Yarbanci.[8][9] Ayyukansa da aka wallafa daga baya sun zama tushen ƙarfafawa ga marubutan nan gaba. Ya kasance memba mai ƙwazo a cikin kwamitocin rubutun Yoruba na shekarun 1966 da 1969. [10] Ya kuma kasance yana da alaka da kungiyar malamai ta Najeriya tsawon shekaru.

A shekara ta 1951, ya lashe kujerar majalisar dokokin yammacin kasar sannan ya zama ministan filaye da kwadago na farko a yankin.[11] Ya kasance shugaban kungiyar Egbado, kuma ya rike mukamin sarauta na Asiwaju na Egbaland.[12]

Ayyukan da aka zaɓa

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Ise ni Ogun Ise ("Aiki maganin talauci")
  • Toju Iwa re Oremi ("Kalli halinka, abokina")
  • Akojopo ewi alâdùn (1961)

Littattafai

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Omo oku orun (1964; "Yar matar da ta rasu")[13]
  • Kuye  (1978)

Littafin karatu

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Aláwìíyé Yoruba Readers (Alawìíyé Yoruba Readers)  (1975)
  1. "Remembering J. F. Odunjo, the literary icon". WN. Nigerian Guardian. Retrieved June 14, 2016.
  2. Albert S. Gérard (1972). "Black Africa, Volumes 2-3". Review of National Literatures. the University of Virginia: St. John's University Press: 195. ISSN 0034-6640. Retrieved June 14, 2016.
  3. Ayọ Bamgbose; Ọlátúndé O. Ọlátúnjí (1986). Yoruba: A Language in Transition. University of Virginia: J.F. Ọdunjọ Memorial Lectures. Retrieved June 14, 2016.
  4. Daily Times of Nigeria Limited (1971). Who's who in Nigeria: a biographical dictionary. Times Press (Magazine Division). Retrieved June 14, 2016.
  5. "Odunjo remembered". Allafrica. Retrieved June 14, 2016.
  6. Janheinz Jahn; Ulla Schild; Almut Nordmann Seilerr (1972). Who's who in African Literature: Biographies, Works, Commentaries. Horst Erdmann Verlag. p. 286. ISBN 978-3-7711-0153-4. Retrieved June 14, 2016.
  7. Albert S. Gérard (1972). Review of national literatures. Black Africa, Volumes 2–3. St. John's University Press. Retrieved June 14, 2016.
  8. Kayode Sobayo (2007). Abeokuta: 175 years of unity & excellence: plus who's who. Skys Production. p. 66. ISBN 978-978-2829-07-8. Retrieved June 14, 2016.
  9. Akínwùmí Íṣọ̀lá (1992). New Findings in Yoruba Studies (J.F. Ọdunjọ memorial lectures series). University of Virginia. ISBN 978-978-30181-4-3. Retrieved June 14, 2016.
  10. Philiip Adédòtun Ògúndèjì. 2016. Odúnjo, Joseph Folàhán. Encyclopedia of the Yoruba, ed. by Tóyìn Fálolá and Akíntúnde Akínyemí, pp. 251,252. Bloomington, IN: Indiana University Press.
  11. Who's who in Nigeria. the University of California: Nigerian Printing and Publishing Company. 1956. p. 212. Retrieved June 14, 2016.
  12. Ayọ Bamgbose; Ọlátúndé O. Ọlátúnjí (1986). Yoruba: A Language in Transition. 1. J.F. Ọdunjọ Memorial Lectures (University of Virginia). p. 5. Retrieved June 14, 2016.
  13. "Literatures in African languages : Yoruba". Encyclopædia Britannica for Kids. Archived from the original on September 28, 2016. Retrieved June 14, 2016.