Jump to content

Kasuwar Sabon Gari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kasuwar Sabon Gari
kasuwa
Bayanai
Farawa 1915
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 12°00′55″N 8°32′24″E / 12.0154°N 8.5399°E / 12.0154; 8.5399
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajihar Kano
Birnijahar Kano
Sabon Gari market

Kasuwar Sabon Gari kasuwa kasuwa ce a birnin Kano, Jihar Kano, Najeriya. An gina ta a cikin shekarar 1914, amma ba a buɗe ba sai 1915.[1]

An kuma ƙirƙiri kasuwar ne saboda Unguwar Sabon Gari dake kusa da kasuwar. Lokacin da aka haɗe lardunan Arewa da Kudu da Legas sai mutanen Kudancin Najeriya suka koma garuruwan Arewa.[2] Tun da akwai al'adu da addinai daban-daban, ya zama da wahala a lokacin haɗuwa da waɗannan baƙin da ƴan ƙasa na asali. Don haka kuma aka zaunar da su a wannan yanki, kuma suna gudanar da harkokinsu a wurarensu. Ta haka aka kafa kasuwar Sabon Gari.

An kuma sake gina shi a karkashin gwamnatin Kano da ginin zamani a shekarar 1983. Kasuwar ita ce babbar kasuwa a Kano.[3] Za a sake gina shi.[4]

  1. "Kundin Tsarin Mulkin Masarautar Kano". www.rumbunilimi.com.ng. Archived from the original on 2022-10-03. Retrieved 2022-09-08.
  2. "Tarihin kasuwanci a Kano (II)". Manhaja - Blueprint Hausa version (in Turanci). 2022-04-27. Retrieved 2022-09-08.
  3. "Kasuwa: Kasuwar Sabon Gari, Kano". VOA. Retrieved 2022-09-08.
  4. Bayero, Muhammad-Hafiz. "KMDMC - Construction of Sabon Gari Market". www.kadunamarkets.com. Archived from the original on 2022-09-30. Retrieved 2023-01-15.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]