Jump to content

Korar bakin hauren Afirka ta Yamma daga Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Korar bakin hauren Afirka ta Yamma daga Najeriya
political slogan (en) Fassara
Yankin najeriya

Batun Korar bakin hauren Afirka ta Yamma daga Najeriya dai, ya biyo bayan umarnin da shugaban ƙasa Shehu Shagari ya bayar a watan Janairun 1983, wanda ya tilastawa baki barin ƙasar ko kuma a kama su. Sakamakon umarnin Shagari, an kori baƙin haure sama da miliyan biyu, ciki har da; yan ƙasar Ghana miliyan ɗaya.[1]

Da yawa daga cikin bakin hauren sun ja hankalin Najeriya ne saboda ƙaruwar man fetur a shekarun 1970, amma a shekarar 1983 tattalin arzikin ya ragu.[2] Ana zargin Shagari ya bayar da umarni ne a kan tashe tashen hankulan da suka dabaibaye sassan ƙasar a shekarar 1980 (wanda aka fi sani da Rikicin Kano ) da wani kuma a shekara ta 1981.[3] Kafin shekarar 1983, korar bakin haure ya sha faruwa a yammacin Afirka saboda wasu dalilai.[4][5] Waɗannan sun haɗa da korar ‘yan Najeriya da Ghana ta yi a shekarar 1954 da 1969 da kuma korar ‘yan ƙasar Najeriya daga ƙasashen Togo, Cote d’Ivoire da Dahomey a shekarar 1958.[4][5]

Sharadi ga bakin haure

[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyar farko zuwa Ghana ta kasance zuwa yamma, ta bi ta Benin da Togo. Saboda yunƙurin juyin mulki a shekarar da ta gabata, shugaban ƙasar Ghana Jerry Rawlings, ya rufe babbar hanyar ƙasarsa da Togo, kuma don kaucewa kwararowar bakin haure, Togo ta kuma rufe kan iyakokinta da Benin. Don haka, da zarar bakin hauren suka isa ƙasar Benin, an takaita hanyar fita kuma an tilasta musu zama a tashar ruwan Cotonou, fadar gwamnatin ƙasar, suna ƙoƙarin neman jirgin ruwa zuwa Ghana. Bayan sun shafe sama da mako guda suna a maƙale, Ghana ta sake buɗe kan iyakokinta, lamarin da ya sa Togo ma ta yi hakan domin 'yan Ghana su koma gida.[2]

Batun Jikka, da aka sani da "Ghana Must Go"

[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu nau'in jakunkuna ne, wanda baƙin hauren ke amfani da jikunkunan wajen kwashe kayansu, ta samu suna laƙanin "Ghana Must Go" a lokacin hijirar. Ya zuwa shekarar 2019, har yanzu ana kiran wannan jakar da wannan sunan a mafi yawan sassan Najeriya, Ghana, da wasu sassan Afirka ta Yamma.[6][7] A shekarar 2020, wani ɗan Najeriya mai ɗaukar hoto Obinna Obioma ya yi amfani da jakunkunan wajen yin kayan sawa da sauran kayayyaki a wani baje kolin tafiye-tafiye mai taken Anyi N'Aga ("Muna Tafiya" a cikin harshen Igbo ).[8]

A duk duniya, jakar tana da wasu sunaye iri-iri da ke danganta ta da baƙin haure. A Jamus ana kiranta "Türkenkoffer" (akwatin Turkiyya), a Amurka, "Chinatown tote", a Guyana, "Samsonite na Guyanese", da sauran wurare daban-daban, a matsayin "Jakar 'Yan Gudun Hijira".[9]

Tasiri kan siyasar zamani

[gyara sashe | gyara masomin]

Dangantaka tsakanin Najeriya da Ghana ta inganta tun a shekarar 1983.[10]

  1. Daly, Samuel Fury Childs (2022-07-30). "Ghana Must Go: Nativism and the Politics of Expulsion in West Africa, 1969–1985". Past & Present. doi:10.1093/pastj/gtac006. ISSN 0031-2746.
  2. 2.0 2.1 Solomonov, M. (2015-08-15). "Ghana Must Go: Exodus From Nigeria Remembered". Yen.com.gh. Archived from the original on 2018-04-25. Retrieved 2017-05-14.
  3. Aremu, J. Olaosebikan (July 2013). "Responses to the 1983 Expulsion of Aliens from Nigeria: A Critique". African Research Review. 7 (3): 340–352. doi:10.4314/afrrev.v7i3.24.
  4. 4.0 4.1 Peil, Margaret (August 1971). "The Expulsion of West African Aliens". The Journal of Modern African Studies. 9 (2): 205–229. doi:10.1017/S0022278X00024903. S2CID 153884282.
  5. 5.0 5.1 Peil, Margaret (Autumn 1974). "Ghana's Aliens". The International Migration Review. 8 (3): 367–381. doi:10.1177/019791837400800303.
  6. "Ghana Must Go: Containing The Mayhem of #Migration". Africa at LSE. 2017-08-14. Retrieved 2019-09-14.
  7. "Ghana Must Go: The ugly history of Africa's most famous bag". www.graphic.com.gh. Archived from the original on 2019-09-05. Retrieved 2019-09-14.
  8. Orjinmo, Nduka (2020-11-19). "In pictures: Turning the iconic Ghana Must Go bag into high fashion". BBC News. Retrieved 2020-11-19.
  9. Hunt, Liz (2007-06-01). "Immigrants have bags of ambition". The Telegraph. ISSN 0307-1235. Retrieved 2019-09-14.
  10. "Ghanaians love to visit these 5 Places in Nigeria". News Ghana. 2017-05-11. Retrieved 2017-05-14.