Maƙera

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maƙera
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Industrial furnace (en) Fassara
Amfani wajen foundry (en) Fassara
makera amma ta zamani
wani makeri tare da yaronsa a makera suna kira
yana kera wani karfe

Makera masana'anta ce ko kuma wuri ne da ake kebancewa don sana'ar sarrafa tama da karafa da zinare da azurfa da sauran su. Sana'ar kira sana'a ce dadaddiya wadda take da dimbin tarihi a kasar hausa kuma kusan makera sune suke kera mafi yawan kayan aikin sana'o'in hannu. Kira ta kasu kashi biyu akwai kirar fari da kuma kirar baki. Ga bayanin su daya bayan ɗaya.

Ire-iren kira[gyara sashe | gyara masomin]

 1. kirar fari: kirar fari anan ne ake kera irin kayan kwalliya/Ado na mata kamar su sarka, dan kunne, kumbo, askar wanzamai da kuma abun hannun mata da dai sauransu [1].
wata babbar makera a birnin Birmingham
 1. Kirar baki: kirar baki ita kusan kira game gari wadda ta hanyar wannan kirar ne ake kira wasu kayan amfani kamar galma ko kuma garma fatanya ko kuma fartanya takobi manjagara da dai sauransu.

Kayan aikin Makera[gyara sashe | gyara masomin]

 1. Uwar Makera: karfe ce dunkulalliya wadda akanta ne ake buga karfe don mai dashi wani abu daban bayan an fito dashi daga wuta
 2. Guduma da ita ake bugun karfen da ake son kerawa bayan an dora shi akan makera
 3. Masaba itama dai abin bugun karfe ce, sai dai ita da zalla karfe ake yinta
 4. Madashi shi kuma da shine huda kota/kota bayan an sa shi a wuta yayi ja-jawur
 5. Gizago dashi ake sassakar kota
 6. Kurfi dashi ake datsa karfe
 7. Gawayi shine makamashin wuta
 8. Zugazugi fata sai ayi mata jima da zugazugi ake hura wutar makera
 9. Araftaki/Awartaki karfe ne da ake daukar karfe daga cikin wuta da kuma rike karfe yayin sarrafa shi
 10. Tama ita kuma tama itace sinadarin da ake yin karfe da ita
 11. Matsoni: dashi ake huda karfe
 12. Kasko ana aje ruwa acikin kasko don tsoma karfe a cikin shi don ragewa karfe zafi
 13. karfe shine abunda ake sarrafawa ko kuma kerawa
 14. Turu a cikin turu ne ake hura wutar makera

Wadannan sune kayayyakin da ake yin kira dasu a makera [2].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-04-17. Retrieved 2021-04-17.
 2. https://m.facebook.com/permalink.php?story_fbid=412713845747551&id=306340003051603&locale2=es_LA