Madatsar Ruwan Ɓagwai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Madatsar Ruwan Ɓagwai
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihajihar Kano
Coordinates 12°10′41″N 8°09′02″E / 12.177957°N 8.150669°E / 12.177957; 8.150669
Map

Watari Dam madatsar ruwa ne dake a karamar hukumar Bagwai a arewa maso yamma ta jihar Kano na Najeriya.[1] [2]

Babban Hoto na Madatsar Ruwan Watari dake Ɓagwai

An gina madatsar ruwa ta Watari tsakanin shekara alif 1977 zuwa shekarar 1980. An gina madatsar ruwan a kan kuɗin Nijeriya Naira ₦ 7,108,000.00. Dam din yana da nisan kilomita 2 daga garin Bagwai da 8km kudu maso yamma da garin Bichi . Tana da fili mai girman hekta 1,959 tare da adadin ruwa kimanin lita miliyan 92.74 [59,60]. Dam din yana tsakanin latitude 12 ° 9'24 "N da 8 ° 8'12" E tare da yanayi biyu daban (rigar da bushe). Lokacin damina wanda yake tsayawa daga watan Mayu zuwa watan Oktoba da kuma lokacin rani yakan wuce daga watan Nuwamba zuwa watan Afrilu. Matsakaicin zafin shekara-shekara, yana tsakanin 16 - 410Cand kuma matsakaicin ruwan sama na shekara-shekara yana zuwa daga 700 - 813mm.

Al’umma suna amfani da madatsar don ayyukan noma a yankin. Akwai gidan ruwa wanda yake aika ruwa daga madatsar zuwa wasu sassa na cikin birnin Kano da sauran garuruwan jihar kamar Bichi da Bagwai.

Ita ce madatsar ruwa ta uku mafi girma a cikin jihar Kano wacce take da karfin adana ruwa kimanin 104.55Mm2. Dalilin gina madatsar ruwan don hana ambaliyar ruwa da ban ruwa, masunta da kuma amfanin na biyu sun hada da samar da ruwa na shakatawa da kuma kiyaye namun daji.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Tasiu, Yalwa Ibrahim (28 December 2014). "Effects of anthropogenic factors on the phytoplanktons distribution of Watari Dam, Kano State". Standard Research Journal.
  2. J. S., Ogutoyin (1991). Meteorological Hazards and Development. Kola Okanlawon Publishers. p. 95.