Masarautar Diriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Diriya
إِمَارَةُ الدِّرْعِيَّةِ الْكُبْرَى (ar)

Suna saboda Saud I (en) Fassara
Wuri
Map
 24°44′00″N 46°34′32″E / 24.733333°N 46.575556°E / 24.733333; 46.575556

Babban birni Diriyah (en) Fassara
Yawan mutane
Harshen gwamnati Larabci
Addini Musulunci
Bayanan tarihi
Mabiyi Emirate of Diriyah (en) Fassara da Bani Khalid Emirate (en) Fassara
Ƙirƙira 1744
Rushewa 9 Satumba 1818
Ta biyo baya Second Saudi State (en) Fassara
Muhimman sha'ani
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati Sarauta
• Shugaban ƙasa Muhammad bin Saud (en) Fassara (1744)

Masarautar Diriya wadda kuma aka fi sani da kasar Saudiyya ta farko, [1] an kafa ta a watan Fabrairu shekara ta alif dari bakwai da ashirin da bakwai 1727 (1139 AH ).</ref> was established in February 1727 (1139 AH).[2][3] A farkon shekarar 1744, sarkin wani garin Najdi da ake kira Diriyah, Muhammad bin Saud, da Sarkin Musulmi na yankin Muhammad bn Abd al-Wahhab sun kulla kawance don kafa wata kungiyar kawo sauyi ta zamantakewa da addini domin hada kan da dama daga cikin jihohin Larabawa. [4]

Abdulllah Bn Saud

Kafuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

Gidan Saudat da na kusa da ita sun tashi da sauri suka zama mafi rinjaye a Larabawa ta hanyar cin nasara a Najd da farko, sannan kuma sun fadada tasirinsu akan gabar tekun gabas daga kasar Kuwait har zuwa kan iyakar kasar Oman . Bayan haka kuma sojojin Saudiyya sun kawo tsaunukan Asir a karkashin jagorancinsu, yayin da Muhammad bn Abd Al Wahhab ya rubuta wa mutane da malamai wasiku don shiga fagen yaqi wato jihadi . Bayan yakin soja da yawa, Muhammad bin Saud ya rasu a shekarar ta 1765, ya bar jagoranci ga dansa, Abdul-Aziz bin Muhammad. Dakarun Saudiyya sun yi nisa har suka samu jagorancin birnin Karbala mai tsarki na Shi'a a shekarar 1801. A nan ne suka rusa wurin ibadar waliyyai da abubuwan tarihi tare da kashe fararen hula sama da dubu biyar 5000. A matsayin ramuwar gayya, wani matashi dan Shi'a ya kashe Abdulaziz a shekarar 1803, bayan ya bi shi zuwa Najd.

Rushewar mulki[gyara sashe | gyara masomin]

Daular Usmaniyya ta bai wa mataimakin sarkin Masar Muhammad Ali Pasha aiki na raunana karfin gidan Saudiyya. Wannan ya fara yakin Ottoman-Saudi, inda Muhammad Ali ya aika da sojojinsa zuwa yankin Hejaz ta hanyar ruwa. Ɗansa, Ibrahim Pasha, sannan ya jagoranci dakarun Ottoman zuwa tsakiyar Nejd, inda suka mamaye gari bayan gari. Magajin Saudat, dansa Abdullah bin Saud, ya kasa hana sake kwace yankin.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. James Norman Dalrymple Anderson. The Kingdom of Saudi Arabia. Stacey International, 1983. p. 77.
  2. "Saudi Arabia to commemorate 'Founding Day' on Feb. 22 annually: Royal order". Al Arabiya English (in Turanci). 27 January 2022. Retrieved 15 February 2022.
  3. "History of the Kingdom | kingdom of Saudi Arabia – Ministry of Foreign Affairs". www.mofa.gov.sa. Retrieved 15 February 2022.
  4. Empty citation (help)