Moors

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Moors
Addini
Musulunci

Moors Musulmai ne mazauna yankin Iberiya, Sicily, sassan Kudancin Faransa, da Arewacin Afirka a Tsakiyar Zamani . A Turai, ana amfani da kalmar sosai don magana akan mutanen da kakanninsu suka kasance Arewacin Afirka .

Moors (Musulman Umayyawa) sun fito ne daga Arewacin Afirka da Siriya. Yawancinsu sun zo ƙasashen da ke yanzu Spain da Fotigal . Suna da tasiri sosai akan al'adun waɗannan ƙasashe.

Musulman Umayyawa su ne suka kame Al Andalus suka sa mata suna Al Andalus, Wanda ke nufin kasar masu barna.