Munzali Jibril
Appearance
Munzali Jibril | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Munzali Jibril ya kasance babban farfesa ne na Ingilishi, kuma tsohon Babban Sakatare na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa. Ya kuma kasance tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Bayero, Jihar Kano, Najeriya. Ya kasance mai kula da makarantar horar da ‘yan sanda ta Najeriya da ke Wudil. Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya nada shi a shekara ta 2010. Yanzu haka shi ne Shugaban-Kwalejin Jami'ar Tarayya ta Lafia.
Jibril ya taba zama shugaban Majalisar Cibiyar Gudanarwar Najeriya. Yayi karatun digirinsa na farko, da kuma digiri na uku a fannin fasaha daga jami'ar Ahmadu Bello, Jami'ar Leeds da kuma Jami'ar Lancaster.[1][2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "NIM elects Professor Munzali President". Text "accessdate" ignored (help); Text "22 February 2021" ignored (help)
- ↑ "Jonathan Appoints Jibril for Police Academy Upgrade". Retrieved 22 February 2021.