Bambanci tsakanin canje-canjen "Arewa 24"
Fixed typo Tags: Reverted Mobile app edit Android app edit |
Tags: Undo Reverted |
||
Layi na 1 | Layi na 1 | ||
([[User:Ihayatu|Ihayatu]] ([[User talk:Ihayatu|talk]]) 22:12, 30 Mayu 2023 (UTC)) |
|||
{{databox}} |
{{databox}} |
||
'''''AREWA24''''' tashar talabijin ce ta tauraron dan adam ta [[Nijeriya|Najeriya]] wacce ake samu a DSTV, GOtv, Startimes,da canal+ wanda ke nuna salon rayuwar [[Arewacin Najeriya|Yankin Arewacin Najeriya]]. Tashar tana daga cikin tashoshi na farko na [[Harshen Hausa|harshen hausa]]. Tashar talabijin ta Arewa 24 tana yaɗa shirye-shiryenta ga masu kallo sama da mutum miliyan 40 a Najeriya da Yammacin Afirka, a cewar tashar wadda ke bikin shekara bakwai da kafuwa. |
'''''AREWA24''''' tashar talabijin ce ta tauraron dan adam ta [[Nijeriya|Najeriya]] wacce ake samu a DSTV, GOtv, Startimes,da canal+ wanda ke nuna salon rayuwar [[Arewacin Najeriya|Yankin Arewacin Najeriya]]. Tashar tana daga cikin tashoshi na farko na [[Harshen Hausa|harshen hausa]]. Tashar talabijin ta Arewa 24 tana yaɗa shirye-shiryenta ga masu kallo sama da mutum miliyan 40 a Najeriya da Yammacin Afirka, a cewar tashar wadda ke bikin shekara bakwai da kafuwa. |
Canji na 22:13, 30 Mayu 2023
Arewa 24 | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | tashar talabijin |
Ƙasa | Najeriya |
Aiki | |
Bangare na | sherin television a najeriya |
arewa24.com |
AREWA24 tashar talabijin ce ta tauraron dan adam ta Najeriya wacce ake samu a DSTV, GOtv, Startimes,da canal+ wanda ke nuna salon rayuwar Yankin Arewacin Najeriya. Tashar tana daga cikin tashoshi na farko na harshen hausa. Tashar talabijin ta Arewa 24 tana yaɗa shirye-shiryenta ga masu kallo sama da mutum miliyan 40 a Najeriya da Yammacin Afirka, a cewar tashar wadda ke bikin shekara bakwai da kafuwa. Tashar wadda ke da babban ofishi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, a ranar Litinin 28 ga watan Yunin 2022, ta cika shekara takwas cur da kafuwa. Arewa 24 tasha ce da ke yaɗa shirye-shiryen da suka shafi rayuwar Hausawa ta yau da kullum cikin harshen Hausa - saɓanin kafofi irinsu BBC Hausa da ke yaɗa labarai kawai. Wata sanarwa daga tashar ta ce an kafa ta ne "domin cike wagegen giɓi" a arewacin Najeriya.[1]
Tarihi
AREWA24 mallakar Equal Access ce kuma tana daukar nauyin shirye-shiryen al'adu da ilimantarwa ga mutanen arewacin Najeriya a cikin harshen hausa. Cibiyar sadarwar tashar ita ce Nilesat. An kirkiro AREWA24 ne a shekara ta 2013 domin cike gurbi a cikin shirye shiryen nishadi da kuma salon rayuwa na harshen hausa. Kaddamarwar ta ci kusan dala miliyan bakwai kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta dauki nauyinta. Tashar ita ce tashar talabijin ta farko da ake gabatar da shirye-shiryenta 24/7 da harshen Hausa wacce ta samo asali daga gina zaman lafiya da nishadi. A cewar shafin yanar gizon Equal Access International, tashar na nufin fadada al'adun Arewacin Najeriya, tare da samar da alfahari da al'adu. A shekara ta 2017, AREWA24 ta yi aiki tare da Eutelsat Communication don bunkasa damarta a matsayin tashar talabijin ta kyauta a yankin Kudu da Saharar Afirka don masu jin Hausa. A shekara ta 2018, tashar ta kara waka da wasanni a cikin harshen hausa. A wannan shekarar, AREWA24 ta kulla sabuwar kawance da kungiyar Girl Effect don tallafawa nasarar 'yan mata a arewacin Najeriya. Tashar ta kuma hada hannu da finafinan Kannywood da ke Kano, Najeriya.[2]
Bikin Cikar Arewa24 Shekara 7 da Kafuwa
Tashar talabijin ta Arewa 24 tana yaɗa shirye-shiryenta ga masu kallo miliyan 40 a Najeriya da Yammacin Afirka, a cewar tashar wadda ke bikin shekara bakwai da kafuwa. Tashar wadda ke da babban ofishi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, a yau Litinin 28 ga watan Yunin 2021, ta cika shekara bakwai cur da kafuwa. Arewa 24 tasha ce da ke yaɗa shirye-shiryen da suka shafi rayuwar Hausawa ta yau da kullum cikin harshen Hausa – saɓanin kafofi irinsu BBC Hausa da ke yaɗa labarai kawai. Wata sanarwa daga tashar ta ce an kafa ta ne “domin cike wagegen giɓi” a arewacin Najeriya. “An kafa tashar Arewa 24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken giɓin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishaɗi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa, waɗanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya da al’adu da kaɗe-kaɗe da fina-finai da fasaha da girke-girke da kuma wasanni.” Shugaban Arewa 24, Jacob Arback ya ce: “Mutane da dama ba su fahimci cewa akwai mutane masu magana da harshen Hausa sama da milyan 80 a Arewacin Najeriya da kuma yankin Sahel ba, kuma yankin na cike da matasa masu basira a ko’ina. “Sai dai abin da na fi alfahari da shi, shi ne yadda hukumar gudanarwa da ma’aikatanmu suka tattaru daga bangarori na rayuwa daban-daban da addinai da ƙabilu da kuma yankunan Najeriya daban-daban.” Tashar na da ɗumbin mabiya a shafukan sada zumunta da suka haɗa da Facebook (1,397,067) da Twitter (124.5K) da Instagram (1.7k). [3]
SHIRYEN-SHIRYEN DA SUKE WAKANA A YANZU
- Gari ya waye
- Dadin Kowa Zango na 3
- Kwana Casa'in Zango na 6
- Fina-finan Kannywood
- H Hip Hop
- Zafafa 10
- Akushi Da Rufi Zango Na biyu
- Ubongo Kids
- Akili & Me
- Mata A Yau
- Kaddarar Rayuwa
- Lafiya Jari
- Labarin (Shiri Mai dogon zongo)
- Waiwaye
Shirin Gari ya waye
Shirin GARI YA WAYE, shiri ne na musamman na Gidan AREWA24 da ke kawo muku a kowacce safiya, shirin yana duba ne ga dukkanin rayuwar Arewacin Najeriya; Al’adu da Wasanni da Matasa da al’amuran dake faruwa yau da gobe na Fasaha da Wasannin Kwaikwayo da Kiwon Lafiya da Motsa Jiki, Zamantakewa, Harkokin Kasuwanci, Nishadantarwa da Jaruman ‘Yanwasa da ma wasun su, Shirye-shiryen Gari ya waye sun hada da Tattaunawa akan muhimman batutuwa da Rahotanni da suka saba zuwa a cikin shirin.[4]
Shirin Akushi da rufi
Shirin Akushi Da Rufi wanda Kwararriyar Mai shirya Abinci kuma mai gabatarwa Fatima Rabi’u Gwadabe, ta ke kawo muku girke-girken Arewacin Nijeriya iri daban-daban da za’a iya gudanarwa a kowanne Dakin Girki. Kowanne shiri yana zuwa mukune da sabon salon girki na musamman daga Arewaci wanda ake gabatarwa cikin sauki da tsari kuma mataki-mataki, dadin dadawa, za’a koyi fasahar girke-girke na gargajiya. Sa’annan, masu kallo zasu san muhimmancin amfani da kayayyakin gina jiki da kuma Sinadaran girki na musamman.
Dadin Kowa
Wasan kwaikwayo na asali mai farin jini da AREWA24 ta shirya, wanda ya lashe lambar yabo, inda ya kawo labarin Dadin Kowa, wani kirkirarren gari wanda jaruman cikinsa suke nuni da irin rayuwar al’ummar dake arewacin Najeriya ta zahiri. Da irin wannan labaran ne masu kallo suke ganin kansu a wannan matsayi da irin burikansu da kalubalensu da kuma kwatanta irin dabi’un su wajen fadi tashinsu wajen yanke shawara game da sana’arsu da iyalansu da kudadensu ko kuma rikici. Dadin Kowa shine ya cinye gasar Afirka Magic na 2016.