Jump to content

Mustapha Badamasi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Mustapha naburaska)
Mustapha Badamasi Naburaska

Mustapha badamasi Wanda akafi sani da na buraska ko nabraska dan wasan kwaikwayo ne musamman fannin barkwanci a Masana'antar Kannywood. An haifi Mustapha ashekarar alif dari tara da tamanin da hudu (1984) a Jihar Kano, Najeriya. Ana kiransa da wannan laƙabine sakamakon zuwansa kasar Amurka inda ya samo lambar yabo a wani gari me suna braskem, sannan yayi fim me suna Naburaska.[1][2]

Mustapha ya gudanar da rayuwarsane a inda aka haifeshi jihar Kano, mahaifinsa malami shikuma Almajiri ne, anan yayi karatun shi na zamani da addini, yana da aure domin yana da mata biyu da yara shida.

Yayi karatun addini da na boko tundaga firamare da sakandare a jihar Kano, Arewacin Najeriya sannan yazo Zariya domin cigaba da makarantar gaba da sakandare inda ya fara karatun jami'a a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Mustapha dan kasuwa ne, dan fim ne, dan siyasa ne. Yafara sana'ar fim/wasan kwaikwayo a shekarar 2001 amma bai shahara ba sai a shekarar 2017, a cikin fim din jarumi nan Adam A Zango mai suna babban yaro Wanda darakta Falalu Dorayi ya bada umarni.

Mukami a gomnatin jihar Kano

[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Janairun shekarar 2022 mai girma gomnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada Mustapha Naburaska a matsayin mai bashi shawara akan labaran farfaganda.[3]

Finafinain jarumin

[gyara sashe | gyara masomin]

Jarumin yayi fina-finai da dama amma wadanda suka shahara sune kamar haka:

  1. wankan sikari
  2. babban yaro
  3. dan gaske
  4. basaja da sauran su.

Sannan yana cikin wani fim mai dogon zango a tashar Arewa24 mai suna gidan badamasi.

  1. "Daga Bakin Mai Ita tare da Mustapha Naburaska". BBC Hausa. 15 July 2021. Retrieved 12 October 2022.
  2. Lere, Mohammed (15 May 2015). "Tag: Mustapha Naburaska". Premiumtimesng.com. Retrieved 12 October 2022.
  3. Khalid, A'isha (30 January 2022). "Ganduje ya gwangwaje jarumi Naburaska da mukami a gwamnatinsa". Legit.hausa.ng.com. Retrieved 12 October 2022.