Nasir Zangon-Daura
Nasir Zangon-Daura | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Nasiru Sani Zangon Daura ɗan siyasan Najeriya ne kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Katsina ta Arewa a majalisar dattawa ta 10. An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Zango/Baure na jihar Katsina a kan tikitin jam'iyyar All Progressives Congress, APC. [1] [2]
Ilimi da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a makarantar Capital, Kaduna, sannan ya halarci kwalejin Barewa da ke Zariya inda ya yi karatun sakandire. Ya yi karatun Form guda shida a Cibiyar Cambridge, London kuma daga baya ya koma Kwalejin Lindisfarne Ruabon. Ya yi karatun digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. [3]
An zaɓe shi a shekarar 2011 zuwa majalissar ƙasa ta 7 domin wakiltar mazaɓar Zango/Baure ta jihar Katsina. An sake zaɓen sa a majalisa ta 8 da ta 9 a shekarar 2015 da 2019 akan tikitin jam'iyyar APC. A lokaci guda a majalisar ya kasance shugaban kwamitin majalisar kan harkokin cikin gida da kuma memba na wasu kwamitoci da dama. [4] A zaɓen majalisar dattijai da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, ya samu kuri’u 174,062 inda ya doke Sanata Ahmed Baba Kaita na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 163,586. [5] [6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Why We Fought On The Floor Of The House Of Reps Today - Zangon Daura | Sahara Reporters". saharareporters.com. Retrieved 2023-04-25.
- ↑ Benjamin, Isaiah (2022-11-22). "2023: Youths Disagree With Zangon Daura Over Support For Presidential Candidate" (in Turanci). Retrieved 2023-04-25.
- ↑ "NASIRU SANI ZANGON DAURA". www.myrep.ng. Retrieved 2023-04-25.
- ↑ kabir (2020-11-11). "Interior Committee Legislators Inspect Facilities at Nigeria Immigration Service". PRNigeria News (in Turanci). Retrieved 2023-04-25.
- ↑ Ibrahim, Tijjani (2023-01-25). "Buhari's senatorial district: Kaita, Daura set for epic battle". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-04-25.
- ↑ "APC sweeps 3 Senatorial seats, 9 Reps in Katsina - P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2023-04-25.