Jump to content

Nestle Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nestle Najeriya
Bayanai
Iri kamfani
Masana'anta Hanyar sarrafa abinci
Ƙasa Najeriya
Aiki
Kayayyaki
Mulki
Hedkwata Lagos,
Tarihi
Ƙirƙira 1969

Suna a hukumance Nestle Nigeria Plc kamfani ne na musamman mai samar da abinci da abin sha wanda ke da hedikwata a birnin Legas. Kamfanin mallakar wani kamfani ne, dake a ƙasar Switzerland kuma yana da alaƙa da kamfanin Tolaram Group. An kafa kamfanin ne a shekara ta 1961 kuma ya gudanar da kasuwancin sa a ƙarƙashin sunan (Nestle Products Nigeria Limited). Kamfanin na da babbar masana'anta a cikin Estate Industrial Estate, Jihar Ogun. Yana samar da (cereal) na karin kumallo, kayan abinci na jarirai, kayan abinci da (hydrolyzed plant protein).

Mujallar Africa Business ta saka sunan kamfanin a matsayin ɗaya daga cikin jerin manyan kamfanoni 100.[1]

Kamfanin ya fara kasuwanci da sunan Nestle Products Nigeria, a cikin shekara ta 1969, an canza sunan zuwa Food Specialties Limited. Ya fara kasuwanci a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya a shekarar 1979 biyo bayan dokar inganta 'yan asalin kasar. A cikin shekara ta 1991, an kuma canza sunan kamfanin zuwa (Nestle Foods Nigeria) daga nan bayan shekaru goma ya sauya suna zuwa, (Nestle Nigeria PLC). Tun da farko, aikin kamfanin shine rarrabawa da kuma sayar da kayayyakin Nestle wanda a baya ƴan kasuwa suke shigo da su a cikin ƙasar daga ƙasashen waje. A cikin 1971, ya inganta kayan ɗan-ɗano na sinadarin Maggi, wanda hakan ya kai kamfanin ga kafa masana'antar tattara kaya a Legas.[2] Kamfanin ya yi hayar filaye a sabuwar Estate Agbara a cikin 1978 kuma bayan shekaru uku ya fara samar da kayayyakin Maggi da Milo. A cikin 1982, an samar da Cerelac a Najeriya daga Agbara. Tsakanin 1984 zuwa 1986, kamfanin ya gabatar da kayayyakin yaye jarirai tare da abubuwan da ke cikin gida mafi girma, wannan ya hada da (Cerelac Maize) da Nutrend, tare da (Mixture of soy and maize).[2] Daga baya ya gabatar da Chocomilo, kayan zaƙi. A cikin shekara ta 2011, kamfanin ya fadada samar da (marquee) tare da bude masana'antar Maggi a Flowergate, jihar Ogun.[3] Nestle Waters Nigeria ta ƙaddamar da wani wurin samar da ruwan sha na al'umma don tabbatar da tsaftataccen ruwan sha a yankin Magedari da ke birnin Abuja wanda wani bangare ne na ƙoƙarin Nestle na tabbatar da samun ruwa mai kyau.[4]

A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin samar da ruwa mai kyau, Manajan Kasuwanci, Nestle, Mrs. Gloria Nwabuike, ta ce sun horar da dalibai sama da 800, malamai 300 a makarantu 140 a jihohin; Legas, Ogun, Osun da kuma babban birnin tarayya.[4]

Talla da rarrabawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Nestle Nigeria ya ɗauki nauyin gasar cin abinci ta kasa ta Maggi, kuma a baya ya ɗauki nauyin wasan nuna girki na Maggi-(Maggi- cooking show). Hakanan ya ɗauki nauyin gasar wasanni ta hanyar reshensa (Milo brand) .

Kamfanin yana da masana'antu guda biyu a jihar Ogun da cibiyar rarraba hajar kamfanin a Ota. Alamomin Nestle kamar Cerelac, Milo, Maggi cube sun sami matsayin sunan cikin gida.[5]

[6]

Abinci da hatsi

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Cerelac
  • Nutrend
  • Golden Morn
  • NAN
  • Lactogen

Kayan Ɗanɗano

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Top 250 African Companies 2017: Recovery proves elusive for Africa's major stocks - African Business Magazine". African Business Magazine (in Turanci). 2017-06-19. Archived from the original on 2018-09-21. Retrieved 2018-09-20.
  2. 2.0 2.1 "Nestle Manufacturing Operations in Nigeria" (PDF). 2011.
  3. "NIGERIA: Nestle opens factory following CHF87m investment." just-food.com, 4 Feb. 2011.
  4. 4.0 4.1 "Nestle inaugurates Abuja community water facility". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2021-02-05.
  5. "Nestle Nigeria PLC - Stronger Profitability Growth Impeded By Rising Operating Costs." All Africa, 6 July 2014.
  6. "Equity research (FSDH)" (PDF). www.fsdhgroup.com. Archived from the original (PDF) on 2018-09-21. Retrieved 2023-02-26.