Jump to content

Nkechi Ikpeazu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nkechi Ikpeazu
Rayuwa
Haihuwa Ile Ife, 1960 (63/64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Okezie Ikpeazu
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
Matakin karatu doctorate (en) Fassara
postgraduate diploma (en) Fassara
Digiri a kimiyya
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Malami, account executive (en) Fassara da gwamna
Mrs._Nkechi_Ikpeazu,_wife_of_the_Governor_of_Abia_State

Nkechi Caroline Ikpeazu (née Nwakanma) ita ce matar Gwamnan jihar Abia na yanzu da ke kudu maso gabashin Najeriya.[1][2]

Kuruciya da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]
Nkechi Ikpeazu

An haifi Nkechi Ikpeazu a ranar 1 ga watan Satumban 1965, a birnin Ile-Ife. Ta fito ne daga Ohanze Isiaha na karamar hukumar Obingwa ta jihar Abia. Ta halarci Makarantu kamar haka; Firamare ta Community Primary School Ohanze; Girls High School, Aba; Teacher Training College Ihie; Kwalejin Alvan Ikoku College of Education Owerri; Jami'ar Enugu State University of Science and Technology Enugu; University of Nigeria Nsukka; jami'ar yanar gizo na National Open University of Nigeria; da kuma jami'ar jihar Abia, Uturu. Tana da shaidar karatu na NCE a fannin Nazarin Kasuwanci (Business Studies), da digiri na farko a fannin hadin kai da ci gaban karkara ( Cooperatives and Rural Development), sannan ta yi karatun difloma a fannin Digiri a fannin Gudanarwa (PGD. Management) sannan kuma ta yi digiri na biyu a fannin Gudanarwa (MSc in Management). Ta kammala digirin digirgir a jami'ar jihar Abia, Uturu.[3][4]

Nkechi ta yi aiki a matsayin mai koyarwa, sannan kuma mai kula da harkokin kudi a Camway Ventures Lagos, ya yi shekara goma yana aikin banki tare da bankin Lobi a tsakanin 1986 da 1996, sannan ya kasance a matsayin Rajistara na Kungiyar Kwadago da Gwamnatin Jihar Abia.[5]

Nkechi mai san cigaban wasanni ce kuma ta kasance babban mai tallafawa kungiyar kwallon kafa ta mata na jihar Abia wato, Abia Angels FC.[6]

Ayyukan Agaji

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta hanyar kungiyar ta mai zaman kanta, Vicar Hope Foundation, VHF, ta gina gidaje da dama ga talakawa. Gidauniyar Vicar Hope Foundation VHF ita ma tana cikin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga uwa da yaro, fada da cutar kansa, ciwon suga, da cututtukan sikila. VHF a halin yanzu ta kammala ginin asibitin sikila / cibiyar gano cutar kansa da cibiyar kula da cutar a birnin Umuahia kuma tana fatan bayar da magani a farashi mafi sauki.[7][8][9] Kungiyar tana da GBV inda ake bada shawarwari kan kariya da magani.

Rayuwar mutum

[gyara sashe | gyara masomin]

Nkechi tana aurn gwamnan jihar Abia na yanzu Dr. Okezie Ikpeazu, wanda ya fito daga Umuobiakwa, karamar hukumar Obingwa. Suna da yara maza biyu da mata biyu. Ikpeazu Deaconess ne na Cocin Seventh Day Adventist kuma alakanta kusanci da Ubangiji.[10]

  1. "Abia Governor's Wife offers scholarship to Alma-maters best student". Vanguardngr.com. 8 July 2015. Retrieved 14 April 2016.
  2. "Ikpeazu's wife seeks strict enforcement of sickle cell law". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 24 June 2020. Retrieved 23 February 2022.
  3. "Mrs. Nkechi Ikpeazu – The wife of the Abia State Governor". Nextzon Business Services Limited. 8 March 2018. Retrieved 20 May 2020.
  4. "Wikipedia, the free encyclopedia". en.wikipedia.org. Retrieved 23 May 2020.
  5. Admin. "Mrs Nkechi Ikpeazu the wife of the Abia state governor". Next Zon. Retrieved 23 January2019.
  6. "Ikpeazu's Wife Lauds Abia Angels". ngrguardiannews.com. 26 October 2015. Retrieved 14 April 2016.
  7. "Nkechi Ikpeazu lifts widows, the blind with houses". ngrguardiannews.com. 9 December 2015. Retrieved 14 April 2016.
  8. "Ikpeazu's wife advocates regular diabetes check". Diabetes UK. 27 November 2015. Retrieved 18 April 2016.
  9. "Abia Governor's Wife offers scholarship to Alma-maters best student". Vanguardngr.com. 8 July 2015. Retrieved 14 April 2016.
  10. Admin. "Mrs Nkechi Ikpeazu the wife of the Abia state governor". Next Zon. Retrieved 23 January 2019.