Jump to content

Oyingbo Market

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kasuwar Oyingbo
Bayanai
Farawa 1920
Ƙasa Najeriya
Kasuwan Oyingbo

Kasuwar Oyingbo wata katafariyar kasuwa ce ta zamani wacce ke cikin Oyingbo, babban birni a yankin Ebute Metta a jihar Legas. Kasuwar tana ɗaya daga cikin mafi daɗewa kuma mafi yawan kasuwanni a Legas inda hakan ke ba da kaso mai tsoka ga tattalin arzikin jihar.[1]

Ciniki a Kasuwar Oyingbo

An kafa kasuwar Oyingbo a farkon shekarun 1920 a matsayin wurin ajiyar kayan amfanin gona. A hankali kasuwar ta faɗaɗa saboda ci gaban da ake samu a yankunan Oyingbo, Ebute Metta da Legas Mainland.[2]

A cikin shekarun 1930, ‘yan kasuwa daga titin Apapa sun koma kasuwar Oyingbo domin kara haɓaka girman kasuwar da nufin mayar da kasuwar babbar cibiyar kasuwanci da za ta jawo hankalin kwastomomi daga kowane ɓangare na Najeriya.[2]

Tsarin asali

[gyara sashe | gyara masomin]

Kasuwar Onyingbo ta ruguje ne a ƙarƙashin gwamnatin shugaban karamar hukumar Legas Island a wancan lokacin a kokarin sake ginata ta zama babbar kasuwa ta hanyar haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu inda suka gayyaci Cif MKO Abiola domin aza harsashin ginin sabuwar kasuwar.[1]

A shekarar 2015, tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, ya ƙaddamar da sabuwar kasuwar da aka saɓunta, bayan kokarin sake gina kasuwar daga wannan gwamnati zuwa waccan.

Sabuwar katafaren kasuwar Oyingbo, gini ne mai hawa hudu da aka gina akan kasa murabba'in mita 504 da filin ajiye motoci kusan 150 a kasa, buɗadɗiyar shaguna 622, shagunan kulle-kulle 102, ofis 48, bandakuna 134 da kofar fita shida. An kiyasta sake gina kasuwar a kan kudi Naira biliyan 1.[2]

  • Jerin kasuwanni a Legas
  1. 1.0 1.1 "Joy as Lagos rebuilds Oyingbo market". Emmanuel Udodinma. The Nation. 1 April 2015. Retrieved 10 July 2015.
  2. 2.0 2.1 2.2 "Lagos commissions new Oyingbo market 24 years after demolition". Wole Oyebade. The Guardian. 15 March 2015. Retrieved 10 July 2015.