Jump to content

Patrick Obi Ngoddy

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Patrick Obi Ngoddy
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 1940 (83/84 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen, Ibo
Karatu
Makaranta California Polytechnic State University (en) Fassara
Michigan State University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Sana'a
Sana'a Malami, Manoma da food engineer (en) Fassara
Wurin aiki Michigan da Ile Ife
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Patrick Obi Ngoddy, Farfesa ne ɗan Najeriya a fannin Injiniyanci da sarrafa Abinci a Faculty of Agriculture University of Nigeria, Nsukka.[1][2][3] Shi ne shugaban majagaba na sashen Kimiyyar Abinci da Fasaha,[4] tsohon shugaban tsangayar aikin gona kuma memba na Kwalejin Kimiyya ta Najeriya.[5]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Patrick Obi Ngoddy a ranar 24 ga watan Yuni, (1940). Ya sami digirinsa na farko a fannin Injiniyanci na Aikin Gona daga Jami'ar Jihar California Polytechnic, San Luis Obispo a shekara ta (1965) a cikin shekarar 1967 izuwa 1969, ya sami M.Sc. da kuma Ph.D. a Tsarin Aikin Noma da Injiniyan Abinci daga Jami'ar Jihar Michigan,[1][6][2] Gabashin Lansing, Michigan bi da bi.[1][6][2]

Ngoddy ya fara aikinsa na ƙwararru a Jami'ar Jihar Michigan a matsayin malami a fannin Injiniyanci n Aikin Noma a shekara ta 1968. A cikin shekarar ta alif 1968, ya zama mataimakin farfesa a Injiniyancin Abinci da Aikin Noma kuma Darakta na Laboratory Control Problem Agricultural a shekarar ta alif 1969.1969.[1][4][6] A shekarar ta (1971) ya dawo Najeriya ( Jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife) inda ya zama Farfesa a fannin Injiniya da sarrafa Abinci a shekarar ta (1978) Ya taba zama Farfesa a fannin Injiniyanci da Sarrafa Abinci na Jami’ar Najeriya Nsukka, inda ya rike muƙamai da dama kamar Sashen Kimiyya da Fasaha na Abinci daga shekarun alif (1979) zuwa 1982, Shugaban tsangayar Aikin Gona daga shekarun 1981 zuwa 1983, Mataimakin Shugaban Jami’a daga shekarun 1985. zuwa 1986, Dean of School of Post-Graduate Student daga shekarun 1985 zuwa 1987 da Mataimakin Shugaban Jami'ar, makarantar kimiyya daga shekarun 1995 zuwa 1998.[1][4][6]

A shekara ta (1965) ya zama Fellow of the American Society of Agricultural Engineers, Fellow Institute of Food Technology (IFT, USA) a shekara ta 1969, memba na American Society for Heating, Refrigeration and Air-Conditioning Engineering (ASHRAE) a shekarar 1970, da Fellow na Kwalejin Kimiyya ta Najeriya.[6][5]

wallafe-wallafen da aka zaɓa

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Ihekoronye, AI, & Ngoddy, PO (1985). Haɗin kimiyyar abinci da fasaha don wurare masu zafi.[7]
  • Uvere, PO, Onyekwere, EU, & Ngoddy, PO (2010). Samar da masara–bambara gyada na karin abinci da aka inganta kafin haifuwa tare da kayan sarrafa abinci mai wadatar calcium, iron, zinc da provitamin A.
  • Uzochukwu, SV, Balogh, E., Tucknot, OG, Lewis, MJ, & Ngoddy, PO (1994). Abubuwan da ba su da ƙarfi na giyar dabino da ruwan dabino.
  • Uvere, PO, Ngoddy, P. O., & Nnanyelugo, DO (2002). Tasirin jiyya na amylase-rich ful (ARF) akan danko na karin kayan abinci.
  • Ngoddy, PO (1972). Rufe tsarin sarrafa sharar gida ga dabbobi. Hukumar Kare Muhalli ta Amurka.
  • Uvere, PO, Ngoddy, PO, & Nwankwo, CS (2014). Hardness as a modification index for malting red and white sorghum (kaffir) grains.[8]
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Food Science and Technology - Staff Profiles". Faculty of Agriculture, University Of Nigeria Nsukka (in Turanci). Retrieved 2023-06-22.
  2. 2.0 2.1 2.2 "NLNGS Science Prize Judges begin adjudication process". Archived from the original on 2023-06-23. Retrieved 2023-12-03.
  3. Reporter, Freedom (2021-03-24). "NLNG's Science Prize judges begin adjudication process for 2021 cycle". Freedom Online (in Turanci). Retrieved 2023-06-22.
  4. 4.0 4.1 4.2 "The Faculty". Faculty of Agriculture, University Of Nigeria Nsukka (in Turanci). Retrieved 2023-06-22.
  5. 5.0 5.1 "Fellowship | The Nigerian Academy of Science" (in Turanci). 2016-10-13. Retrieved 2023-06-22.
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 6.4 J. E., Obiegbuna; C. S, Anarado; C. C, Ezegbe, eds. (2021). Importance and application of Psychrometry in Food Processing. Festschrift in honour of Engr. Prof. Patrick Obi Ngoddy At 80 Promethean commentaries with seminal Paper contributions, tributes and biographical sketch. Macmillan. ISBN 979-978-985-480-6 Check |isbn= value: checksum (help).
  7. A. I., Ihekoronye; P. O, Ngoddy (1985). Integrated food science and technology for the tropics. Macmillan. London: Macmillan. ISBN 9780333388839.
  8. P. O, Uvere; P. O, Ngoddy; C. S, Nwankwo (2014). "Hardness as a modification index for malting red and white sorghum (kaffir) grains". Journal of the Science of Food and Agriculture. 94 (5): 890–897. Bibcode:2014JSFA...94..890U. doi:10.1002/jsfa.6331. PMID 23900972.