Jump to content

Sharks FC

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sharks FC
Bayanai
Iri ƙungiyar ƙwallon ƙafa
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Port Harcourt
Tarihi
Ƙirƙira 1972
Dissolved 2016
sharks-fc.com

Sharks FC tsohuwar ƙungiyar kwallon kafa ce a Najeriya dake garin Fatakwal a jihar Rivers. Sun taka leda a babban rukuni a wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya, a gasar Firimiya ta Najeriya. Filin wasan gidansu shine filin wasa na Sharks ko da yake sun buga wasu manyan wasanninsu a filin wasa na Liberation. A cikin shekarar 2016, kulob ɗin ya haɗe a hukumance tare da abokan hamayyar Dolphins FC kuma ƙungiyoyin biyu sun zama gama gari da ake kira Rivers United FC.

Ƙungiyar Sharks ta kusa ƙaura zuwa Abeokuta a cikin shekara ta 1998, saboda matsalolin jama'a. A wata zanga-zanga, sun rasa wasanni shida na ƙarshe na 1998 Professional League, sun gama kakar a mataki na kasan teburi, a gasar da maki 32 kuma an dakatar da su na tsawon shekaru biyu.[1]

Sun fara kakar 2009-10 da rashin taɓuka abin kirki, sun koma zuwa mataki na kasan teburi, kuma suna tafiya ƙarƙashin jagorancin manajoji uku lokacin da Kadiri Ikhana ya bar kungiyar bayan yayi wasanni takwas da kungiyar. A ranar 27 ga watan Fabrairu 2010 ƙungiyar gasar da su ke bugawa, ta dakatar da su har abada saboda "rashin bin ka'idoji" bayan zabtare ma'aikatan gudanarwar su. Hakan ya biyo bayan fashi da makami ne a jihar Edo a kan hanyarsu ta dawowa daga wani ƙaramin sansanin da ke Abuja. Sun yi nasarar kammala kakar shekarar a matsayi na 16 da maki 48, inda suka kaucewa fadawa matakin-(fita daga buga wasan kungiyar a kaka mai zuwa) wato relegation kenan a turance, da maki ɗaya.

Haɗewa tare da Dolphins

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan da aka dawo daga gasar a shekarar 2016, gwamnatin jihar Rivers ta haɗe ƙungiyar Sharks FC da abokan karawarta Dolphins FC inda suka kafa kungiyar Rivers United FC wacce ta ɗauki Dolphins a gasar firimiya.[2]

Nasarorin da aka samu

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Gasar Zakarun Kungiyoyin Afirka ta Yamma (Kofin UFOA)
    • Masu nasara (1): 2010
  • Kofin FA na Najeriya
    • Wadanda suka yi nasara (3): 1979, 2003, 2009

Bayanan kula

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Nigeria 1998". RSSSF.
  2. "Dolphins renamed Rivers United Football Club | Goal.com". www.goal.com.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]