Shehbaz Sharif

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shehbaz Sharif
Firimiyan Indiya

3 ga Maris, 2024 -
Anwar ul Haq Kakar (en) Fassara
23. Firimiyan Indiya

11 ga Afirilu, 2022 - 13 ga Augusta, 2023
Imran Khan - Anwar ul Haq Kakar (en) Fassara
President of the Pakistan Muslim League (N) (en) Fassara

13 ga Maris, 2018 -
Nawaz Sharif (en) Fassara
Chief Minister of Punjab (en) Fassara

8 ga Yuni, 2013 - 8 ga Yuni, 2018
Najam Sethi (en) Fassara - Hasan Askari Rizvi (en) Fassara
President of the Pakistan Muslim League (N) (en) Fassara

2009 - 2011
Ch Nisar Ali Khan (en) Fassara - Nawaz Sharif (en) Fassara
Chief Minister of Punjab (en) Fassara

8 ga Yuni, 2008 - 26 ga Maris, 2013
Dost Muhammad Khosa (en) Fassara - Najam Sethi (en) Fassara
Chief Minister of Punjab (en) Fassara

20 ga Faburairu, 1997 - 12 Oktoba 1999
Mian Muhammad Afzal Hayat (en) Fassara - Parvez Elahi (en) Fassara
Member of the 15th National Assembly of Pakistan (en) Fassara


District: NA-132 Lahore-X (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Lahore, 23 Satumba 1951 (72 shekaru)
ƙasa Pakistan
Harshen uwa Harshen Punjab
Ƴan uwa
Mahaifi Muhammad Sharif
Abokiyar zama Tehmina Durrani (en) Fassara
Yara
Ahali Nawaz Sharif (en) Fassara
Yare Sharif family (en) Fassara
Karatu
Makaranta St. Anthony's High School (en) Fassara
Government College University (en) Fassara
Harsuna Harshen Punjab
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Wurin aiki Islamabad
Imani
Addini Mabiya Sunnah
Jam'iyar siyasa Pakistan Muslim League (N) (en) Fassara
IMDb nm14635898
cm.punjab.gov.pk

Mian Muhammad Shehbaz Sharif ( Urdu : میاں محمد شہباز شریف‎ ,Template:IPA-hnsAn haife shi (ranar 23 ga watan Satumba shekarar 1951) ɗan siyasar ƙasar Pakistan ne kuma ɗan kasuwa wanda a yanzu haka shine firaministan ƙasar na 24 tun a watan Maris 2024, ya kuma riƙe wani muƙamin a baya daga watan Afrilun shekarar 2022 zuwa watan Agustan shekarar 2023. Shi ne shugaban kungiyar musulmin Pakistan (PML-N). A baya a fagen siyasarsa, ya zama babban ministan Punjab sau uku, wanda ya sa ya zama babban ministan Punjab mafi daɗewa a kan karagar mulki.

An zaɓi Shehbaz a Majalisar Lardi ta Punjab a shekarar 1988 da kuma Majalisar Dokokin Pakistan a 1990. An sake zaɓen shi a Majalisar Dokokin Punjab a 1993 kuma aka naɗa shi Shugaban Ƴan adawa. An zaɓe shi a matsayin babban minista na lardin Punjab mafi yawan jama'a a Pakistan, a karon farko a ranar 20 ga Fabrairun shekarar 1997. Bayan juyin mulkin da akayi a Pakistan a shekarar 1999, Shehbaz tare da iyalansa sun kwashe shekaru suna gudun hijira a Saudiyya, inda suka koma Pakistan a shekara ta 2007. An naɗa Shehbaz babban minista a karo na biyu bayan nasarar da PML-N ta samu a lardin Punjab a babban zaben Pakistan na shekarar 2008. An zaɓe shi a matsayin babban ministan Punjab har sau 3 a babban zaɓen 2013 ya na kan muƙamin har saida aka kayar da jam'iyyar shi a babban zaɓen 2018. A wannan lokacin a matsayin sa na babban minista, Shehbaz ya samu damar yin suna a matsayin shugaba mafi zama abin koyi a mulkin sa. Ya qaddamar da manyan ayyuka na ababen more rayuwa a Punjab kuma an san shi da ingantaccen shugabancinsa. An zabi Shehbaz a matsayin shugaban kungiyar Muslim League-N na Pakistan bayan an hana dan uwansa Nawaz Sharif daga mukaminsa sakamakon shari'ar Panama Papers. Bayan zaɓen 2018 ne aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Jam’iyyar.

A watan Disamba na 2019, Hukumar Kula da Laifuka ta Kasa (NAB) ta daskarar da wasu kadarori 23 mallakar Shehbaz da dansa Hamza, inda ta zarge su da karkatar da kudade. A ranar 28 ga Satumba, 2020, NAB ta kama Shehbaz a Babban Kotun Lahore kuma ta tuhume shi kan zargin satar kuɗi. An tsare shi a gidan yari kafin a yi masa shari'a. A ranar 14 ga Afrilu, 2021, Babban Kotun Lahore ta sake shi kan belinsa game da almundahana. A ranar 12 ga Oktoba, 2022, an sallami Shehbaz da Hamza bisa dukkan tuhume-tuhume na almundahana da kuma karkatar da kudade da babbar kotu ta musamman da ke Lahore ta yi. A cikin rikicin siyasar Pakistan na 2022, Majalisar Dokoki ta kasa ta zabi Shehbaz a matsayin Firayim Minista a ranar 11 ga Afrilu 2022 bayan yunkurin rashin amincewa da Imran Khan. A ranar 12 ga watan Agustan shekarar 2023 ne dai majalisar ta tsayar da aiki saboda cikar wa'adin shekaru biyar. Domin samun karin lokaci na zabe da sauran nasarorin siyasa, Shehbaz da kawancen PDM sun amince da rusa majalisar a ranar 9 ga watan Agustan 2023, wanda shugaban Pakistan ya amince da shi

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]