Shinzo Abe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Shinzo Abe
Shinzō Abe Official.jpg
Rayuwa
Haihuwa Shinjuku-ku (en) Fassara, Satumba 21, 1954 (66 shekaru)
ƙasa Japan
Mazaunin Prime Minister's Official Residence (en) Fassara
Harshen uwa Harshen Japan
Yan'uwa
Mahaifi Shintarō Abe
Mahaifiya Yōko Kishi
Siblings
Karatu
Harsuna Harshen Japan
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Tsayi 175 cm
Muhimman ayyuka Solidarity Against the North Korean Threat (en) Fassara
Towards a Beautiful Nation (en) Fassara
Mamba Nippon Kaigi (en) Fassara
Imani
Addini Shinto (en) Fassara
Jam'iyar siyasa Liberal Democratic Party (en) Fassara
IMDb nm2606053
www.s-abe.or.jp/
Shinzo Abe

Shinzō Abe (安倍 晋三 Abe Shinzō, IPA: [abe ɕin(d)zoː]; An haife shi a 21 ga watan Satumba shekara ta 1954, shahararren dansiyasa kuma firayim minista na 63rd na kasar Japan kuma shugaban jam'iyar Leader of the Liberal Democratic Party (LDP) tun daga 2012, kafin nan shine na 57th dake rike da ita tun daga shekara ta 2006 zuwa 2007. shine firayim minista na uku da suka fi kowa dadewa akan karagar mulki tun bayan yakin Japan.[1]

Mai Daraja Shinzō Abe 安倍 晋三, Shine Firayim minista na 57th a Kasar Japan maici a yanzu. Ya kama aiki daga 26 ga watan December shekara ta 2012 har zuwa yau, kuma Sarkin Kasar ta Japan shine Akihito, Mataimakinsa shine Tarō Asō.

Tarihinsa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haife da rada masa suna 安倍晋三 (Abe Shinzō) a 21 ga watan September shekara ta 1954 (shekarunsa 64) Tokyo, Japan Jam'iyar sa, Liberal Democratic Matansa: Akie Matsuzaki (m. 1987) Wurin zamansa: Kantei Makarantar sa: Jami'ar Seikei. Abe yataso ne daga gidan yan'siyasa kuma an zabe shine a matsayin firayim minista na farko tun a watan satumban shekara ta 2006. A lokacin yana da shekara 52, yazama firayim minista mai karancin shekaru a kasar Japan tun bayan yakin Kasar kuma firayim minista na farko da aka Haifa bayan yakin duniya II. Abe yayi marabus a dalili na rashin lafiya a 12 ga watan September 2007, bayan kuma jam'iyarsa tayi rashin nasara a zaben kansiloli a wannan shekara. Yasuo Fukuda ne yagaje shi, Wanda na daya daga cikin firayim minista biyar da suka kasa dawowa ofishinsu fiye da watanni 16. Abe ya dawo siyasa a 26 ga watan September shekara ta 2012, ya doke abokin takarar sa tsohon Ministan Tsaron Kasar, Shigeru Dan fafatwa a shugaban cin Kasar na jam'iyar LDP. Bayan samun nasara a jam'iyar ne a zaben 2012, yazama firayim minista na farko daya sake dawowa karagar mulki tun bayan Shigeru Yoshida a shekara ta 1948. An sake zabarsa a shekarar 2014 kuma da sake samun 2 cikin 3 na masu yawan al'ummah tare da abokin gamayyarsa Komeito, kuma yakara samun haka a zaben 2017.[1]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]