Yaƙin Duniya na II

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Yakin duniya II)
Jump to navigation Jump to search
Yakin Duniya na II
WW2Montage.PNG
world war
MabiyiYakin Duniya na I Gyara
followed bySecondo dopoguerra italiano Gyara
start time1 Satumba 1939 Gyara
end time2 Satumba 1945 Gyara
participantAxis, Allies Gyara
has causeTreaty of Versailles, causes of World War II, Hitler Gyara
has effectBritish Pet Massacre Gyara
Regensburg ClassificationNQ 2545 - NQ 2795 Gyara
tarihin maudu'itimeline of World War II, diplomatic history of World War II Gyara
described at URLhttps://stadtlexikon.karlsruhe.de/index.php/De:Lexikon:ereig-0074 Gyara
Stack Exchange taghttps://history.stackexchange.com/tags/world-war-two Gyara
maintained by WikiProjectWikiProject World War II Gyara
category for mapsCategory:Maps of World War II Gyara
WWII.jpg

Yaƙin Duniya na 2 da turanci World War II akan kintse rubutun kamar haka WWII ko WW2, har wayau ana kiran shi da turanci Second World War. Yaƙin duniya dai wani yakine da duniya baki daya suka afka a ciki wanda ya kwashi tsawon shekaru shida (6) ana gwabzawa, tun daga shekara ta 1939 har zuwa shekarar 1945. Mafiya yawan kasashen duniya tare da ƙasashe masu ƙarfi sune suka ja daga a tsakanin su, inda suke yaƙan juna: Hakane ya haifar da gagarumin gumurzu tsakaninsu wanda akalla mutane sama da miliyan ɗari ne (100,000,000) suka tsunduma a ciki daga kasashe sama da talatin (30). Mafiya yawan ƙasashen da suka shiga cikin yaƙin sun saka dukkan tattalin arzikin su, da Masana'antunsu da ilimin su na kimiyya da fasaha don ganin sun yi galaba a yaƙin. Yaƙin duniya na II shine yaki mafi muni a duniya wanda Dan'adam bai taba gani ba, inda aka samu rasa rayukan mutane daga miliyan 50 zuwa miliyan 85, yawan cinsu fararen kaya ne daga Kasar Soviet Union wato Rasha ayanzu da kuma Kasar Sin. An sami kashe-kashe, kisan kiyashi akan Yahudawa, tsarin jefa bama-bamai, mutuwa sanadiyar yunwa da cututtuka, da kuma amfani da makamin kare-dangi a yakin Nuclear Weapon.

Ansoma yakin ne daga ranar 1 ga watan Satumba 1939 zuwa 2 Satumba 1945 tsawon shekaru (6 da kwana daya 1 )

Kasashen kawance sunyi nasara, an kifar da Gwamnatin Nazi dake Jamus, An samu faduwar Daulolin yankin Japan dana Italiya, Anfara amfani da Makamin kare dangi wato Atomic weapons, Inganta ayukka da jiragen sama,rusa kungiyar League of Nations,kirkirar Majalisar Dinkin Duniya wato United Nations, Fara ƙiyayya tsakanin Kasar [[Amurka[] da Rasha, fara yakin mummuƙe wato Cold war. Jagororin ƙungiyar ƙawance na Kasa da kasa,

  • Kwamandodi da Shuwagabanni
  1. Soviet Union Joseph Stalin
  2. United States Franklin D. Roosevelt
  3. United Kingdom Winston Churchill
  4. Jamhoriyar Sin (1912–1949) Chiang Kai-shek

Wa 'yanda ake fada dasu

  1. Nazi Germany Adolf Hitler
  2. Masarautar Japan Hirohito
  3. Masarautar Italy Benito Mussolini

Abubuwan da akayi asaransu An kashe Sojoji: Sama da miliyan 16,000,000 An kashe farin kaya: Sama da miliyan 45,000,000 Adadin rayukan da aka rasa: Sama da miliyan 61,000,000 (1937–1945)

ƙasar Japan da ke son ta mamaye nahiyar Asiya da yankin Pacific, ta fara yaƙi da Kasar Sin tun daga 1937 duk da cewar babu bangaren da yafito a fili ya ayyanar da yaki akan wanin sa. Ana dai ganin yakin ya soma ne a 1 ga watan Satumbar 1939, bayan mamaye ƙasar Poland da ƙasar Jamus tayi, da kuma ƙaddamar da yaki da Kasar Faransa, Ingila sukayi akan kasar Jamus a karshen shekara ta 1939 har zuwa farkon shekara ta 1941, sai da irin gumurzu da shirin da Jamus din tayi ne, hakan yasa ta samu nasara da mallakar kusan duka nahiyar Turai, kuma sai suka kulla ƙawance da kasar Italiya da Japan (Axis powers) a karkashin yarjejeniyar Molotov–Ribbentrop Pact of August 1939, Jamus da ƙasar Soviet sun rarraba tare da mallakar yankunan Turai na kasashe kamar irin su Poland, Finland, Romania da jihohin dake Baltic. Bayan fara yaƙi akan kasashen dake yankin Afirka ta arewa da Afirka ta gabas, da kuma faduwar kasar Faransa a tsakiyar shekarar 1940. Yaƙin ya koma mafi yawanchi tsakanin Kasashen Jamus,Italiya da kuma Daular Romania akan Daular Biritaniya. Sai kuma fara Yaƙi a Balkans,Da kuma Fafatawar sararin samaniya a Ingila wato Aerial Battle of Britain da kuma harin sama tare dayin ruwan bomabomai da ƙasar Jamus din tayi wa Birtaniya wato Blitzkrieg, sai kuma fafatawar Mallakar Tekun Atlantik da ya biyo baya, Ana Chikin wannan Bala'in ne sai kuma Kasashen haɗakar (Axis Powers) a turai suka ƙaddamar da hari akan kasar Soviet Union wato Rasha a ranar 22 june 1941 , hakan yasa suka bude wani sabon shafin yaƙin mafi muni a tarihi,A kuma watan December 1941, Japan ta kaddamar da wani hari a kasar Amurka da wasu yankunan turawa dake yankin tekun Pacific. Hakane yasa kasar ta Amurka ta ƙaddamar da yaƙin akan ƙasar Japan, kuma ta samu goyon bayan kasar Biritaniya, amma sai kasashen dake ƙawance da Japan na turawa suma suka mara wa Japan din baya, hakane yasa Japan ta ƙwace yawancin yankunan turawa dake yankin tekun Pacific, wanda yawancin kasashen Asiya suke ganinsa a matsayin wani shiri ne daga kasashen yamma na yin mamaye a yankunan su, amma kuma baya ƴan kwanaki da suka gane wa idanuwan su irin zalunchin da Axis Powers keyi yasa dagabisani ra'ayin mutanen ƙasashen ya juya akan su. Yaki ya tsaya a shekara ta 1945 bayan Japan ta miƙa wuya, kuma Jamus da Italiya suma anyi galaba akamsu a arewacin Afirka da gabashin ta, da kuma gagarumar nasarar da Red Army suka yi akan jamus da Italiya a garin Stalingrad dake Soviet Union a shekarar 1943, da kuma mamaye Sicily da Italiya, da nasarar kasashen kawance (Allied Powers) a yankin Pacific, a 1944, kasashen kawance sulun kwace yankin Faransa daga hannun Jamus kuma itama kasar Soviet Union ta dawo da yankunanta daga hannun Jamus da ƙawayenta. Sa'annan kuma a shekarar 1944 zuwa 1945 kasar Japan ta sha kashi sosai a yankin Asiya, musamman fafatawar da suka yi da Amurka a Tekun Pacific wato Battle Of Midway,da kuma tsakiyar kasar Sin da kasar Burma, hakan ya sanya su rasa dukanin yankunan da suka mamaye.

Yaki a nahiyar turai ya ƙare ne sanadiyar mamaye Jamus da ƙasashen kawance da ƙasar Soviet suka yi wanda yakai ga kama garin Berlin da mutuwar Adolf Hitler da mika wuyan da Jamus tayi a 8 May 1945. Bayan Potsdam Declaration daga kungiyar ƙawance a 26 July 1945.

ƙin da kasar Japan tayi na mika wuya, yasa ƙasar Amurka ta jefa mata Makamin ƙare dangi wato atomic bomb a garuruwan Hiroshima da Nagasaki a 6 da 9 ga watan Augusta. Da kuma mamaye tsibirin archipelago imminent, da ganin irin asarar rayukan da ake yi, da kuma mamayen yankuna da kasar Soviets ta ke chi gaba dayi a garin Manchuria da tsibirin Kuril dake arewacin kasar ta Japan, hakan yasa Sarkin ƙasar japan wato Hirohito a 2 ga watan satumba 1945 ya mika wuya, wannan ya bada damar yin nasarar sojojin ƙawance a nahiyar Asiya, sai kuma aka fara tuhumar kasar Jamus da japan akan laifukan yaƙi a kotun International Military Tribunal (IMT) da kuma The International Military Tribunal For The Far East ko kuma (IMTFE).

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Wannan ƙasida guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.