Takamba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Takamba
Nau'in kiɗa da type of dance (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Tuareg music (en) Fassara da rawa

Takamba kiɗa ne da raye-raye na asalin ƙabilar Songhai da Abzinawa na Nijar da Mali . Abu ne na kida da rawa. Mawakan suna buga kayan gargajiya da aka fi sani da Kurbu ko Tehardent da kuma Calabash na gargajiya na Afirka . Rawar Takamba ta kuma ƙunshi motsi masu kayatarwa da raye-raye da aka yi duka a zaune da kuma tsaye inda kafaɗa da hannaye ke rawar jiki tare da kwararar kiɗan.[1][2][3][4]

Asalin[gyara sashe | gyara masomin]

Kiɗa da raye-rayen Takamba sun samo asali ne daga Daular Songhai . Kafin a san shi da Takamba, ƴan ƙabilar Abzinawa makiyaya da maƙera ne suka yi ta don nuna farin ciki da ƙarshen girbi mai kyau, faranta wa mayaka da suka dawo daga yaƙi da kuma yaba wa iyalai masu daraja. Griot a wurin zama, zai buga ngoni ko kuma wanda Abzinawa suka fi sani da "tehardent". Kalmar 'Takamba' tana da ilimin asali daga yaren Songhai wanda a zahiri yana nufin "ɗauka".

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Super Khoumeisa Group, fatcard Records, retrieved 2021-02-23
  2. Andy, Morgan (2010), Super Onze de Gao, retrieved 2021-02-23
  3. Gao – Soirée culturelle 'Takamba pour la Paix', MaliActu.net, 2014, archived from the original on 2020-10-23, retrieved 2021-02-23
  4. Takamba, the other desert blues, afropop.org, 2014