Tecno Mobile

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tecno Mobile
Bayanai
Iri ƙaramar kamfani na
Masana'anta consumer electronics (en) Fassara
Aiki
Kayayyaki
Mulki
Hedkwata Shenzhen
Mamallaki Transsion Holdings
Tarihi
Ƙirƙira 2006
Wanda ya samar

tecno-mobile.com


Tecno Mobile kamfanin ƙera wayoyin hannu ne na ƙasar Sin da ke Shenzhen, China.[1] An kafa shi a shekara ta 2006. Wani reshe ne na Transsion Holdings.

Kamfanin na Tecno ya mayar da hankali kan kasuwancinsa a majiyoyin Afirka, Gabas ta Tsakiya, Kudu maso Gabashin Asiya, Kudancin Asiya, Latin Amurka, da kasuwannin Gabashin Turai.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara ta 2006, an kafa kamfanin Tecno Mobile a matsayin Tecno Telecom Limited, amma daga baya ya canza suna zuwa Transsion Holdings tare da Tecno Mobile yana aiki a matsayin ɗaya daga cikin rassansa. A cikin 2007, kamfanin Tecno ya ƙirƙiri tambari na biyu, Itel wanda aka sayar a Afirka. A farkon 2008, Tecno ya mayar da hankali ga Afirka gaba ɗaya bayan binciken kasuwa, kuma zuwa 2010, yana ɗaya daga cikin manyan samfuran wayar hannu guda uku a Afirka.[2]

A cikin 2016, Tecno ya shiga dillancin wayar hannu na kamfanin a Gabas ta Tsakiya.[3] A cikin 2017, ya shiga kasuwannin Indiya, inda ya ƙaddamar da samfurin wayoyinsa na 'Made for India': jerin 'i' - i5, i5 Pro, i3, i3 Pro da i7. Kamfanin ya fara dillancin sa a jihohin Rajasthan, Gujarat, da Punjab, kuma a watan Disamba 2017 ya bazu a faɗin kasar.

Kamfanin ya gano wasu kasuwanni masu tasowa, ban da Afirka da Indiya, masu yawan jama'a amma akwai ƙarancin cinikayya hajar sa a wuraren. Har wayau bai tsaya nan ba, ya kutsa kasuwannin Bangladesh da Nepal a cikin 2017 kuma ya fara gwajin sayar da hajarsa a Pakistan.[4] Har yanzu kamfanin na ƙoƙarin kutsawa cikin kasuwar Pakistan kuma ya fara siyar da hajarsa ta yanar gizo-(online) ta hanyoyin kasuwanci ta Intanet-(E-commerce).

Wayoyin da ake ƙerawa[gyara sashe | gyara masomin]

Wayoyin hannu na Tecno da ake sayarwa a Indiya, ana ƙera su a masana'antar Noida (U.P.).[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Deck, Andrew (2020-06-23). "Your guide to Transsion, Africa's biggest mobile phone supplier". Rest of World (in Turanci). Retrieved 2020-08-08. Transsion operates three brands from its headquarters in Shenzhen in China: Infinix, Itel, and Tecno.
  2. "Samsung, Apple, Tecno top list of mobile brands with highest SOV in Q2 of 2016" (in Turanci). Retrieved 2017-08-26.
  3. "Chinese phone maker Tecno Mobile forays into Middle East". Retrieved 1 October 2017.
  4. "How Transsion became No 3 in India by solving oily fingers problem". South China Morning Post (in Turanci). Retrieved 2018-01-15.
  5. "Transsion Holdings to shift manufacturing base to India".

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]