Titilope Gbemisola Akosa
| Rayuwa | |
|---|---|
| Cikakken suna | Titilope Gbemisola Ngozi Akosa |
| Haihuwa | Lagos,, |
| ƙasa | Najeriya |
| Harshen uwa | Yarbanci |
| Karatu | |
| Makaranta |
University of California, Berkeley (mul) Jami'ar, Jihar Lagos |
| Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
| Sana'a | |
| Sana'a |
lauya, Malamin yanayi da environmentalist (en) |
Titilope Gbemisola Akosa, da aka fi sani da Titilope Akosa, (an haife ta a Legas, Najeriya) masaniyra muhalli ne Na Najeriya, mai ba da shawara kan Adalci na yanayi, lauya, ƙwararre a jinsi da zamantakewar al'umma, kuma Mai fafutukar kare hakkin dan adam. Ita ce ta kafa kuma darakta mai zartarwa ga ƙungiya non-governmental sustainability organization Centre (C21st). Ta jagoranci kamfanin lauya Titi Akosa & Co Nigeria . [1] A shekara ta 2015, ta kasance mai magana da yawun mata da kungiyoyin da ba na gwamnati ba a Yarjejeniyar Yanayi ta Paris ta 2015 a kan batun 'Towards a Gender Responsive Green climate fund in Africa'.[2]
Rayuwa ta farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Titilope Ngozi Akosa kuma ta girma a Jihar Legas, Najeriya. Tun tana ƙarama, ta halarci makarantar firamare da sakandare a Jihar Legas. A lokacin da ta zauna a Jihar Legas, sai ta shiga Jami'ar don karatun gaba da sakandare. Akosa ta kammala karatu daga Jami'ar Jihar Legas, Najeriya inda ta sami digiri na farko na shari'a (LL.B) da Barrister-at-Law (B.L) daga Makarantar Shari'a ta Najeriya a shekarar 1992. Ta kuma sami digiri na biyu a Law (LL.M) daga Jami'ar Legas Najeriya a shekarar 1996. A matsayinta na mae digiri a shari'a, Titilope Akosa mai'kaciyar shari'a ce fagen shari'ar farar hula da aikata laifuka kuma Mai fafutukar kare hakkin dan adam. Ta yi musharaka cikin darussan daban-daban da horo wadanda suka hada da; Darussan membobin tarayya, Cibiyar masu sulhu, Burtaniya, reshen Najeriya, Legas, Najeriya a watan Afrilu na shekara ta 2004, Kulawa da Gudanarwa da aka gudanar a Laberiya ta Forum For African Women Educationalist (FAWE), Kenya a watan Agusta, shekara ta 2006.[1]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Titilope Akosa ta fara ne a matsayin lauya bayan kammala karatunta da kuma kiranta zuwa kotun Najeriya. Ta ci gaba ta in da ta buɗe kamfanin lauya na Titi Akosa & Co tare da wasu abokan aikinta. Ta yi aiki a matsayin shugaban da kuma mai ba da shawara kan shari'a kan 'yancin ɗan adam da na mata, jinsi da canjin yanayi. Akosa ta fara kungiyar da ba ta gwamnati ba don 'Centre for 21st Century Issues' (C21st) Najeriya kuma ta zama mai kula da ayyukanta.
Ta kuma shiga cikin wani aikin da International Alliance of Indigenous Tribal Peoples of the Tropical Forests ta yi a kan wani shirin da aka lakafta Indigenous Network for change project (IPNC), inda ta saka idanu da lura da hanyoyin GEF da kuma yadda suke da alaƙa da 'yan asalin ƙasar. Ta ce ta shigarta cikin shirin IPNC ya zama sillar shigarta cikin ƙwararrun ƙwararrun kan batutuwan 'yan asalin Afirka ta Yamma.[3][1]
Fafutuka
[gyara sashe | gyara masomin]Titilope Akosa a halin yanzu tana aiki a kan fara shawarwarin aikin, tara kudade da saka idanu a aikin yau da kullun na kungiyarta. Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan shari'a da kuma mai ba da horo ga kungiyoyin ƙasa da na duniya a Najeriya da kasashen waje. Har ila yau, tana yin kamfen ɗin ƙaddamarwa, wayar da kan jama'a da kuma fafutuka game da jinsi da canjin yanayi. Har ila yau, tana taimaka wajan gudanar da daidaita shirye-shirye a ƙarƙashin kamfen ɗin fafutuka kan horar dan ƙwarewa ga masu yanke shawara, ƙungiyoyin farar hulla da sauran Masu ruwa da tsaki game da kula da muhalli, da jinsi da canjin yanayi. Ta yi kira ga haƙƙin ilimin yara mata a Najeriya da kuma cewa gwamnatin Najeriya ya kamata ta yi duk abin da ya dace don tabbatar da sakin 'yan matan Chibok da Dapchi da suka ɓace waɗanda Boko Haram ta sace.
- 1 2 3 "Titilope Ngozi Akosa". Global Issues. 21 September 2015. Retrieved 8 May 2020. Cite error: Invalid
<ref>tag; name "Akosa" defined multiple times with different content - ↑ "Does Paris Climate Accord hang Women, Indigenous People". Juan Cole. 21 December 2015. Retrieved 8 May 2020.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>tag; no text was provided for refs namedISSUU