Jump to content

Uche Chukwumerije

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Uche Chukwumerije
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015 - Mao Ohuabunwa
District: Abia North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Abia North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
Ike Nwachukwu
District: Abia North
Rayuwa
Haihuwa Ogoja, 11 ga Janairu, 1939
ƙasa Najeriya
Mutuwa Abuja, 19 ga Afirilu, 2015
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Ciwon huhun daji)
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Uche Chukwumerije (11 Janairu 1939 – 19 Afrilu 2015), wanda aka fi sani da “Comrade Chukwumerije[1] ” saboda gwagwarmayar sa,[2] an zaɓe shi a matsayin Sanata a Tarayyar Najeriya a watan Afrilun 2003, mai wakiltar gundumar Abia ta Arewa.[1]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Chukwumerije a ranar 11 ga watan Janairun 1939 a Ogoja,[3] a Jihar Kuros Riba ta Najeriya a yau, ga Sajan Ogbonna Chukwumerije (wanda aka fi sani da Sarji) da matarsa ta uku Mrs Egejuru Chukwumerije, dukkansu sun fito daga Isuochi a Jihar Abia ta Najeriya a yau. Shi ne na 4 a cikin ƴaƴan mahaifiyarsa su takwas: Daniel, Roland, Ahamefula (Joe), Ucheruaka, Ifeyinwa, Rosa, Ochi, Onyekozuoro (Onyex).

Ya halarci Makarantar Methodist Central, Nkwoagu, Isuochi, Jihar Abia, 1943–52; Makarantar Sakandaren Uwargidanmu, Onitsha, 1953–57; Jami'ar Ibadan, 1958-61, inda ya karanci fannin tattalin arziki;[4] Faith Bible College, Sango-Ota, 1991-92.[5]

Farkon aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaban Features Desk, DailyTimes, 1961; Desk News, Nigerian Broadcasting Corporation (yanzu FRCN);

Fagen siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Chukwumerije ya yi ministan yaɗa labarai da al'adu a ƙarƙashin Janar Ibrahim Babangida[2] da kuma a ƙarƙashin gwamnatin wucin gadi ta ƙasa ta Ernest Shonekan.[3]

Majalisar Dattawa

[gyara sashe | gyara masomin]

A jamhuriya ta hudu, an zabi Chukwumerije a matsayin ɗan majalisar dattawa a tsarin jam’iyyar Peoples Democratic Party, amma ya kasa amincewa da shugabancin jam’iyyar a lokacin da ya ƙi amincewa da ajandar wa’adi na uku. Daga karshe Chukwumerije ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Progressive Peoples Alliance a shekarar 2006, kuma aka sake zaɓen shi a majalisar dattawa a ranar 28 ga watan Afrilu, 2007.[5]

An sake zaɓen Chukwumerije a jam'iyyar PDP a zaɓen watan Afrilun 2011.[6]

Chukwumerije ya auri Gimbiya Gloria N. Iweka. Sun haifi 'ya'ya takwas:[7][8] Che Chidi (1974-), Kwame Ekwueme (1975-1995), Azuka Juachi (1976-), Dikeogu Egwuatu (1979-), Chaka Ikenna (1980-), Uchemruaka Obinna ( 1982-), da tagwayen Kelechi Udoka (1983-) da Chikadibia Yagazie (1983-). Chukwumerije da Gimbiya Iweka sun rabu a 1988. Daya daga cikin ƴa'ƴansu Chika ya samu lambar tagulla a gasar Olympics ta 2008 da aka yi a birnin Beijing.[6] Wani da, Dike, fitaccen marubucin Najeriya ne, mai magana da yawun jama'a kuma mawaƙin wasan kwaikwayo.[9]

Ya mutu a ofishi sakamakon ciwon huhu a shekara ta 2015.[10]

  1. 1.0 1.1 Emmanuel, Ogala (2015-04-19). "How Senator Uche Chukwumerije died - Family - Premium Times Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2020-01-22.
  2. 2.0 2.1 "RIOTING ERUPTS IN NIGERIA OVER CANCELLATION OF VOTE". Washington Post (in Turanci). ISSN 0190-8286. Retrieved 2021-03-10.
  3. 3.0 3.1 "Senator Chukwumerije dies of cancer - P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2022-07-25.
  4. "Revealed: Senator Uche Chukwumerije – How He Passed On and Who He Was!". Nigerian Voice. Retrieved 2022-09-02.
  5. 5.0 5.1 Emmanuel, Ogala (2015-04-19). "How Senator Uche Chukwumerije died -- Family". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-07-25.
  6. 6.0 6.1 ORJI UZOR KALU (10 April 2011). "Orji Kalu Fails; Abaribe, Chukwumerije, Nwaogu Reelected Senators". Online Nigeria. Archived from the original on 28 July 2011. Retrieved 2011-04-20.
  7. vivianonuorah (2015-05-01). "MEET LATE SEN. UCHE CHUKWUMERIJE'S 7 KIDS". Vivys Archive (in Turanci). Retrieved 2022-09-03.
  8. Awa, Omiko (2011-12-28). "WELCOME TO OMIKO AWA'S BLOG: Chukwumerije… The Senator and his taekwondo clan". WELCOME TO OMIKO AWA'S BLOG. Retrieved 2022-09-03.
  9. "Dike Chukwumerije". THE GREEN INSTITUTE (in Turanci). Retrieved 2022-09-03.
  10. "Sen. Chukwumerije dies at 75" (in Turanci). Retrieved 2017-12-22.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]