Umamah Yar Zainab
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Makkah, |
Mutuwa | Jeddah, 686 |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Abu al-Aas dan al-Rabiah |
Mahaifiya | Zainab yar Muhammad |
Abokiyar zama |
Sayyadina Aliyu Q20381119 ![]() |
Yara |
view
|
Ahali |
Ali ibn Zainab (en) ![]() |
Yare | Ahl ul-Bayt |
Sana'a | |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Umamah Yar Zainab 'Yar Abi al-'Āṣ 'Dan al-Rab Ta kasance jika a gun Annabi Muhammad (SAW) da Khadija Yar Khuwailid, ta hanyar 'yarsu Zaynab, don haka kuma ake kiranta da Umāma bint Zainab. Muhammadu kakanta ne na wajen uwa, don haka ita ma Ahlul Baiti ce.Kuma ta kasance daya daga cikin sahabban Annabi Muhammad (S.A.W).
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ita ce 'yar Abu al-As bn al-Rabi', wanda ya auri 'yar Muhammad (SAW.) Zainab, wadda ta kasance yar uwa ga Rukayya, Ummulkulsum, da Fatima.[1]
Lokacin Ummama tana karama, Muhammad (SAW.) ya kasance yana daukar ta a kafadarsa yana sallah. Ya kasance yana ajiye ta ta yi sujada sannan ya sake dauke ta yayin da ya tashi[1]: 27, 163 Muhammad ya taba yin alkawarin ba wa "Wanda na fi so." Matansa sun sa ran zai ba Aisha, amma ya mika wa Umma. A wani lokaci na dabam, ya ba ta zoben zinariya da ya zo daga Sarkin Abyssiniya.[1]: 27–28, 163–164.
Antinta Fatima ta bukaci mijinta Ali akan mutuwarta ya auri ‘yar ‘yar uwarta Umama saboda Umama tana da tsananin shakuwa da soyayya ga ‘ya’yan Fatima Hasan, Ummu Kulthum, Zainab da musamman Husaini.[2] Hilal (wanda aka fi sani da Muhammad al-Awsat ko kuma Muhammad mai tsakiya)[3]: 12 da Awn, dukkansu sun mutu a Iran, tare da kashe na karshen a yakin da suka yi da Qays bn Murra (gwamnan Khorasan), kuma na farko yana mutuwa ta dabi'a[4]. Ana zaton Hilal ya haifi da, mai suna Abu Hashim Abdullah ibn Muhammad, amma ba a san makomarsa ba[5].
Ali ya yi shahada a shekara ta 661, kuma Mu’awiya na daya ya yi wa Ummama shawara. Ta tuntubi al-Mughira bn Nawfal bn al-Harith a kan haka. Ya ce kada ta auri “Dan mai hanta (Hind bint Utba)” kuma ya yi mata tayin magance matsalar. Da ta yarda sai ya ce: “Ni zan aurar da ke da kaina.”[1:28] Wannan auren ya haifar da da namiji guda Yahaya. Babu tabbas ko tana da zuriya bayan wannan. Umama ta raka al-Mughira zuwa gudun hijira a al-Safri. Ta mutu a can c. 680, amma kuma an ce ta rasu a shekara ta 670 (50H).[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 Al-Basri Al-Hashimi, Muhammad ibn Sa'd (1995). Kitab al-Tabaqat al-Kabir [The Women of Madina] (in Arabic). Vol. 8. Translated by Bewley, Aisha. London, the U.K.: Ta-Ha Publishers.
- ↑ Al-Tabari, Muhammad ibn Jarir (1998). The History of al-Tabari. Vol. XXXIX: Biographies of the Prophet's Companions and Their Successors. Translated by E. Landau-Tasseron. Albany, New York, the U.S.A.: State University of New York Press.
- ↑ Al-Basri Al-Hashimi, Muhammad ibn Sa'd (2013). "The Companions of Badr". Kitab al-Tabaqat al-Kabir (in Arabic). Vol. 3. Translated by Bewley, Aisha. London: Ta-Ha Publishers.
- ↑ "Mohammad Hilal Ibn Ali". www.helal.ir. Archived from the original on 2011-07-20.
- ↑ "پایگاه اطلاع رسانی آستان مقدس حضرت محمد هلال بن علی(ع) - Content". Archived from the original on 2011-07-20. Retrieved 2011-03-10.
- ↑ Lammens, H. (1912). Fatima et les Filles de Mahomet (in French). Rome, Italy: Sumptibus Pontificii Instituti Biblici. p. 127.