Jump to content

Jeddah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jeddah
جدة (ar)


Wuri
Map
 21°32′34″N 39°10′22″E / 21.5428°N 39.1728°E / 21.5428; 39.1728
Ƴantacciyar ƙasaSaudi Arebiya
Province of Saudi Arabia (en) Fassarayankin Makka
Governorate of Saudi Arabia (en) FassaraJeddah Governorate (en) Fassara
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 4,697,000 (2021)
• Yawan mutane 860.26 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 5,460 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Red Sea
Altitude (en) Fassara 12 m
Tsarin Siyasa
• Gwamna Saleh Al-Turki (en) Fassara (27 ga Yuli, 2018)
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 21000
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+03:00 (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho 12

Jeddah ko Jiddah ko kuma Jedda; da larabci|جدة, Birni ne dake Tihamah a yankin Hejaz dake gabar Kogin Maliya kuma shine babban birni a yammacin kasar Saudiya. Itace mafi yawan al'ummah a Makkah Province [1], kuma itace keda babban tashar Ruwa a kogin Maliya, tanada adadin mutane kusan miliyan hudu (4,000,000,) tun a kidayar a shekara ta 2017. Kuma itace gari na biyu mafiya yawan al'ummah a kasar Saudiya bayan birnin Riyadh. Jeddah itace cibiyar kasuwancin kasar Saudiya.[2]

Jeddah ce mashigar garin Mecca da Medina, garuruwa biyu masu tsarki a addinin musulunci, kuma garuruwan yawon bude ido.

Dangane da tattalin arziki, Jeddah tana fuskantar Karin cigaba wurin sanya jari a abubuwan dasuka shafi kimiyya da kyerekyere dan tazamo kangaba a kasar ta Saudiya dama yankin gabas ta tsakiya.[3] ansanya Jeddah na hudu a biranen kasar Afirka da Gabas ta tsakiya masu kirkire kirkira a shekara ta 2009 a jerin sunayen birane dake kirkiran sabbin abubuwa.[4]

Jeddah nadaya daga cikin biranan shakatawa a kasar Saudiya kuma ansanyata a cikin kasashe masu kyawu, daga cibiyar nan na Globalization and World Cities Study Group and Network (GaWC). Kasantuwar garin a gabar teku yasa mafi yawan abincinsu yazama kayayyakin ruwa ne, da al'adar da kuma kamun kifi, wanda bazaka ga hakan asauran garuruwan Saudiya ba. Da larabci taken birnin itace "Jeddah Ghair," fassara wato "Jeddah daban ce." Hakane yasa taken mafiya yawan al'ummah garin da yanwaje suke amfani dashi. Ana ganin birnin Jeddah a matsayin garin dayafi tarbar kowa da kowa a kasar Saudiya.

Asalin Sunan da Rubuta shi

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai bayanai biyu da akayi aka samo asalin sunan da yadda ake rubuta shi wato Jeddah, kamar yadda Jeddah Ibn Al-Qudaa'iy, the wanda shine Shugaban Quda'a clan. Cewar sunan ansamo sane daga جدة Jaddah , Kalmar Larabci ce dake nufin "grandmother". Kamar yadda eastern folk sukai imani, Kabarin Eve, Wanda ake ganin itace grandmother of humanity yana nan ne a garin Jeddah.[5] Hukumar addinin garin sun rufe kabarin ne da ginin kankare a shekara ta1975 duk saboda Musulmai masu yin sallah a wurin.

Matafiyi Berber nan Ibn Battuta yaziyarci Jeddah lokacin tafiyarsa na Duniya a 1330. Ya rubuta sunan birnin a littafin sa da "Jiddah".[6]

Hukumar Foreign and Commonwealth Office na Biritaniya da wasu rassuna na gwamnatin Biritaniya sunfi amfani da tsohon spelling din "Jedda", Wanda yasaba da na yadda yake a Turanci ayanzu, amma a shekara ta 2007, spelling ya canja zuwa "Jeddah".[7]

T. E. Lawrence yaji cewar duk wani sunayen Larabci zuwa English was arbitrary. Acikin, Revolt in the Desert, Jeddah is spelled three different ways on the first page alone.[8]

A hukumar gwamnatin Saudiya littafin ta da maps din birnin duk suna dake da sunan ne a rubutu da "Jeddah", wanda ake amfani dashi ako ina a hakan.

  1. Cite web|url=https://www.stats.gov.sa/sites/default/files/ar-makkah.pdf%7Ctitle=population[permanent dead link] of the administrative region of Makkah|last=|first=|date=|website=General authority of statistics|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=
  2. cite news|title=The Saudis may be stretching out the hand of peace to their old foes|url=https://www.economist.com/news/middle-east-and-africa/21728686-rapprochement-iran-may-be-pushing-it-saudis-may-be-stretching-out%7Caccessdate=10[permanent dead link] September 2017|work=The Economist|date=7 September 2017
  3. Cite web |url=http://ae.zawya.com/story.cfm/sidZAWYA20100727050049/comment |title=Archived copy |access-date=2010-07-28 |archive-url=https://archive.is/20120701183223/http://ae.zawya.com/story.cfm/sidZAWYA20100727050049/comment |archive-date=2012-07-01 |dead-url=yes |df=
  4. cite web|author=|url=http://www.innovation-cities.com/emerging-middle-east-africa-city-index/ |title=2thinknow Innovation Cities™ Emerging 11 Index 2009 - Middle East, Africa and Former USSR States | 2009|publisher=Innovation-cities.com |date=2009-11-12 |accessdate=2011-04-17
  5. Jayussi, Salma; Manṣūr Ibrāhīm Ḥāzimī; ʻIzzat ibn ʻAbd al-Majīd Khaṭṭāb Beyond the Dunes I B Tauris & Co Ltd (28 April 2006), p. 295. ISBN|978-1-85043-972-1 [1]
  6. Ibn Battota's Safari. Tuhfat Al-Nothaar Fe Gharaa'ib Al-Amsaar. Chapter: "From Cairo to Hejaz to Tunisia again". ISBN|9953-34-180-X
  7. British Embassy website[permanent dead link] dead link|date=June 2016|bot=medi cbignore|bot=medic
  8. "Lost in translation." Brian Whitaker. Guardian (UK). 10 June 2002.
Asiya    

Kasashen tsakiyar Asiya l

KazakystanKyrgystanTajikistanTurkmenistanUzbekistan

Gabashin Asiya

SinJapanMangoliaKoriya ta ArewaKoriya ta KuduJamhuriyar Sin

Yammacin Asiya

ArmeniyaAzerbaijanBaharainGeorgiaIrakIsra'ilaJordanKuwaitLebanonOmanQatarSaudiyyaSiriyaTurkiyaTaraiyar larabawaFalasdinuYemen

Kudu maso gabashin Asiya

BruneiKambodiyaIndonesiyaLaosMaleshiyaMyanmarFilipinSingaforaThailandTimor-LesteVietnam

Tsakiya da kudancin Asiya

AfghanistanBangladashBhutanIndiyaIranMaldivesNepalPakistanSri Lanka

Arewacin Asiya

Rasha