Waƙoƙin Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Waƙoƙin Gargajiya

Kamar dai yadda kowacce al'ada ko Kabila ta ke da mawakanta, to ita ma kabilar Hausa ta na da na ta mawakan, wadanda su ka yi wakoki masu tarin yawa, cikin hikimomi da basira mara adadi.

Wasu daga cikin mawakan, sun yi wakoki daban-daban, wasu kuma jigon wakokin nasu iri daya ne. Akwai mawakan Sarakuna, akwai na Sha'awa, akwai na Manoma ko 'Yan Dambe ko 'Yan Kasuwa, da dai sauransu.

Mawakan Gargajiya Daga Najeriya[gyara sashe | gyara masomin]

Garaya abin kiɗan gargajiya a Arewacin Najeriya
Masu busa Algaita a Arewacin Najeriya

Wannan sunayen wasu ne daga shahararrun mawakan gargajiya, matattu da kuma rayayyu daga Nijeriya. Mafi yawancinsu dai sun riga mu gidan gaskiya.

Mawakan Gargajiya Daga Kasashen Ketare[gyara sashe | gyara masomin]

Da yake shi Harshen Hausa ya yadu sosai, daga Nijeriya zuwa Niger, zuwa Kamaru, Ghana, Saliyo, Benin da sauransu. Hakan ta haifar da samuwar mawaka da Hausa a wadannan Kasashen da ma tsallake.