Walaaeldin Musa Yagoub Muhamed ( Larabci: ولاء الدين موسى يعقوب ; an haife shi a ranar 1 ga watan Janairu shekara ta 2000) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Sudan wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin mai gaba ga Hay Al-Arab SC .
Yaqoub ya zura kwallo a ragar Mauritania a ranar 17 ga Watan Junairu na shekarar 2018, bayan shekaru biyu bayan ya zura kwallo ta farko a kasarsa a gasar cin kofin CECAFA ta 2015 . [1]