Jump to content

Yarbawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Yarabawa)
Yarbawa

Jimlar yawan jama'a
47,000,000
Yankuna masu yawan jama'a
Benin, Najeriya, Togo, Ghana da Kanada
Harsuna
Yarbanci
Addini
Kiristanci, Musulunci da Addinin Yarabawa
shigar yarbawa namiji
Wasu yarbawa
wani Sarkin yarbawa
Kwamutin yarabawa

Yarbawa mutanen yankin kudancin Najeriya ne masu magana da harshen Yarbanci, a matsayin harshen, ko yaren gado; wato harshen uwa ko harshen haihuwa. Dukkan Yarabawan da ke duniya, sun fito ne daga kaka ɗaya rak; wato tushen su guda ne wanda shi ne Oduduwa.[1]

tambarin yarbawa
abincin yarbawa

Ƙabilar Yarabawa, suna ɗaya daga cikin manya-manyan ƙabilun Afirka ta Yamma (Biobaku, babu shekara). Mutane ne masu son junansu da kuma haɗin kai a tsakanin su. Suna da zaman lafiya da kuma matuƙar karɓar baƙi bakin gwargwado.

Fitaccen masanin tarihi, Dakta Babatola a shekarar (2019) yana kuma da ra’ayin cewa samuwar daɗaɗɗe kuma tsararren shugabanci guda ɗaya tilo, mai tushe guda; Oduduwa, ƙarƙashin sarautar gargajiya shi ne abin da ya ƙara danƙon zumunci a tsakanin Yarabawa duk kuwa da fantsamuwar su zuwa wasu sassan Afirka da ke wajen Ƙasar Yarabawa da ma wasu sassan duniya.[2]

Washington (2016), da Ogunbado (2003), sun yi ƙiyasin cewa sama da mutane miliyan talatin ne suke magana da wannan harshe a ƙasashen Afirka da kuma Brazil. Ogunbado (2003) ya ƙara da cewa sannan kuma akwai mutane sama da miliyan ɗaya da suke magana da wannan harshe a ƙasashe irin su Cuba da Birtaniya da sauran su.[3]

Kenan, muna iya cewa a bias ƙiyasi yanzu akwai Yarabawa a duniya sama miliyan talatin ɗaya. Ile-Ife ce babbar hedikwatarsu a gargajiyance sannan kuma Ooni-Ife shi ne babban sarkinsu tare kuma da cewa Oduduwa shi ne kakansu wanda dukkan Yarabawa daga gare shi suka fito, (Lange, 1995; Babatola, 2019; Babalola, 2017).

Su wane ne Yarabawa?

[gyara sashe | gyara masomin]

[4]Masana harkokin al'adu da na cewa duk da gauraya al'adu irin na zamani amma ba su sanya ƙabilar Yarbawa sun yi watsi da al'adunsu da suka gada tun iyaye da kakanni ba.

To sai dai da yawa daga 'yan wannan ƙabila na cewa tsatsonsu sun fito daga wani mutum da ake kira Oduduwa har zuwa lokacin da ya kafa gari da a yanzu ake kira Ile-Ife - sai dai wasu daga cikinsu na ja da cewa Oduduwa shi ne mafarin tarihinsu.

Da yawa daga kabilar Yarbawa sun yi imani cewa tarihinsu ya faro daga fitaccen jarumi da ake kira Oduduwa wanda kuma garin Ile-Ife ke a mazauni farkon matsugunninsu.

Kuma har kwanan gobe ana yi wa Oduduwa ganin jajirtaccen bil'adama kuma fitila ga sayensu haske kuma ga tafarkin kabilar Yarbawa.

Yarbawa dai na da ɗumbin kayayyakin tarihi da al'adu, suna da Obatala wanda ke a matsayin ubangijinsu.

To sai dai sakamakon wanzuwar addinin Musulunci da Kiristanci da wayewa ko bakin al'adu daga Turai, an samu raguwar kamanta Allah da wani abu da kuma tsagwaron al'adunsu na gargajiya.

Oduduwa kamar yadda masana tarihi suka nuna na cewa Lamaruzu shine mahaifin Oduduwa - ya fito daga kasashen gabas- har ma ake yi masa kirari da cewa Lamaruzu na yamma da Makka. Ya karaso Ile-Ife da jama'arsa wajajen karni na hudu.

Cikin Kabilar Yarbawa akwai wadanda suka yi imani cewa Oduduwa mutum ne, wasu kuwa na cewa ba shine tushen wannan kabila ba. Sai dai har kwanan gobe ana yi masa kallon uban ko mafarin duk wani da ya fito daga ƙabilar Yarbawa.

Basarake Oba Hammed Adekunle Makama, shi ne sarkin garin Olowu-Kuta mai daraja ta daya a jihar Osun, haka nan kuma tsatso ne daga zuria'r Oduduwa.

Sunansu na asali shi ne Yoruba , wanda shi ne sunan da suke kiran kansu da shi, babu bambanci tsakanin mutum ɗaya da kuma jama’u; wato mutane da yawa. Sannan kuma suna yi wa kansu laƙabi da kuma Omo Yoruba , wanda ke da ma’ana ta ɗan Yarabawa ko kuma ‘ya’yan Yarabawa da kuma Omo Oduduwa shi ma da ma’ana ta ɗan Oduduwa ko kuma ‘ya’yan Oduduwa. Haka na ma a Turance Yoruba ake kiran su da shi.

A Ghana da Salo (Sierra Leon) sunansu Aku . A Togo kuma Nagot ko Anago . Ƙasar Barazil kuma sunansu Lucumi . Sai kuma Bahaushe da yake kiran jama’unsu da Yarabawa, mutum ɗaya kuma ya ce Bayarabe .

Fitattun marubuta tarihin Yarabawa (Boahen, Ajayi da Tidy, 1986; Longe, 1995; Johson, 1960; Babatola, 2019; Wardwell, Drewal, Permberton III da Aboidun, 1989; Biobaku; Babalola, 2017; Ogunbado, 2008) sun gamsu cewa asalin Yarabawa abu guda ne; dukkaninsu jikokin Oduduwa ne.

Johnson (1960), Ogunbado (2008) da Babalola (2017) sun hikaito Muhammadu Ballo (1779 - 1837) yana danganta tushen Yarabawa da Lamarudu ɗan Kan’ana mutumin Iraƙi.

Sai dai, Boahen, Ajayi da Tidy (1986), sun saɓa da waccar ruwaya ta Muhammadu Ballo inda suka ce Yarabawa mutane ne waɗanda dama tun asali suke zaune a wannan matsugunni da suke a yanzu tsawon dubunnan shekaru da suka shuɗe bisa la’akari da abin da bincike ya tabbatar daga shi kansa harshen Yarabancin da kuma kimiyyar tarihi (Archeology).

Al'adun Yarbawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Yarbawa sun yi fice ta fuskar raya al'adu kamar a lokacin biki ko suna ko a sa'ilin auratayya har ma da rabon gado.

Al'adarsu ta auratayya na zuwa da biyan sadaki- to amma kuma in namiji ko saurayi ya ga budurwar da yake so, to a maimakon ya fada mata kai tsaye' sai ya je ya fada wa iyayensa domin a yi masa iso gun iyayen budurwa.

Akasari iyaye na bayar da gudunmowa game da wadanda 'ya'yansu za su aura.

Dalilin haka kuwa ya zo domin kauce haduwa da miyagun ƙaddarori kamar na ciwon hauka ko wasu cututtuka ko tsinuwa da mai yiwuwa akwai su a cikin zuri'ar matashin ko budurwar da yake so ya aura.

Ana raye-raye da ruguntsumin raya al'adu bilhakki.. Sai dai a yanzu ana gauraya su da wasu tsare-tsare da zamani ya zo da su.

Sun nuna shi kansa addini wani ɓangare ne daga cikin al'adunsu - saboda haka ake la'akari da fifita al'adu kuma suke ci gaba da tasiri cikin al'amuransu na yau da kullum.

Sai dai kuma ana samun sauyi nan da can sakamakon shigowar addinin Musulunci da na Kirista da kuma shigowar Turawan mulkin mallaka a yankunansu.

Yarabawa, sun rarrabu zuwa jinsi-jinsi ko karye-karye (Kare-Kare) da yawa, amma muhimmai daga cikin su su ne: Ife, Ijesha, Ijamo, Efon, Ondo, Idoko, Igbomina, Egba, Oyo, Ekiti, Akoko, Awori da kuma Ado, (Johnson, 1960; Babalola, 2017).

Sai kuma Babatola (2019), da ya kasafta Yarabawa zuwa: Ife, Ijesha, Ile Ipetu, Ila Orangun, (Osun) da kuma Igbominainbwanɗada ke zaune a jahar Osun; Edo da kuma Itsekiri a jahar Edo; Ekiti a jahar Ekiti; Ondo, Owo, Ikale, Ilaje, Akoko, Akure da Idanre a jahar Ondo; Awori, Eko, Egba da Ijebu a jahar Lagos; Egba, Ijebu, Remo, Yewa/Egbado da Awori a jahar Ogun; Oyo, Ibadan, da (Oke Ogun) a jahar Oyo.

Shi kuwa Biobaku, wanda yake dakta ne a fannin tarihi sannan kuma shugaban Shirin Nazarin Tarihin Yarabawa a Najeriya (Director of the Yoruba Historical Research Scheme, Nigeria), cewa ya yi ana samun Yarabawa a Yankin Yamma (Asalin Ƙasar Yarabawan kenan); da kuma kaɗan a Yankin Arewacin Najeriya; Dahomey (Kwatano kenan); Togo, ƙasar da ake kiran su da suna 'Nagot' ko 'Anago ’. Itsekiri da ke Yammacin Najeriya kuma faɗaɗawa ce ta Yarabawa; Sarkin Bini (Oba of Benin) da zuriyarsa, asalinsu daga Ile-Ife ne, garin Yarabawa mafi tasiri. Haka nan kuma ana samun jinsin Yarabawa a Freetown da ke ƙasar Salo (Sierra Leone), ƙasar da ake kiran su da suna Aku. Haka nan ma akwai Yarabawan Barazil waɗanda ake kira da suna Lucumi.

Daga ina Oduduwa ya fito?

[gyara sashe | gyara masomin]

Masana tarihi kamar Dr. Muhammad Musa Maitokobi ya ce, kamar yadda bincike ya nuna Oduduwa ya fito daga kasashen gabashi ne- sai dai ana tankiya cewa ba za yi garajen cewa wannan kasa ko waccar ba.

Wasu alkaluma na tarihi na nuni da cewa akwai alaka mai karfi ta al'ada a tsakanin kabilar Yarbawa da Barebari musamman kan wasu al'adu da suke kamanceceniya.

"Domin kuwa shi Lamaruzu wanda shi ne uban Oduduwa, ya fito daga kasashen gabas ne - tarihi ya nuna tare suke da Barebari- wannan ne ya sa ake yi masa kirari cewa Lamuruzu na yamma da Makka.

''Hakanan kuma akwai al'adu da yawa wadanda sun yi dai-dai da al'adunsu wadanda kabilun biyu suke da kamanceceniya kamar 'hatta Gunda da ake maganarta ta bangaren Barebari, Yarbawa ma suna da ita.

''Akwai wani Girke na ganguna irin nasu wadanda ake kakkafasu a kasa, duk suna da irinsu.

''Suna da son juna da rashin kar na gaza, kar kuma mu bari dan uwanmu ya gaza sun tafi iri daya. Akwai wata rijiya a nan cikin gidan sarautar Ile-Ife; tana nan da akwai sarka.

''A sani na irin wannan rijiyar akwai ta a wani kauye da ake kira Gazargamu a tsakanin Bultuwa da Subdu -da Galdiram inda yake mai tarihi.

To ina ce yamma da Makka, yamma da Makka gabadaya dai tun daga Maiduguri yamma da Makka ne,'' in ji Dr Maitakobi.

Malam Abdulkabir Bayerabe ne, ya ce duk da addinin Musulunci da na Kirista sun ratsa kabilar Yarbawa, to amma har kwanan gobe ba su yi watsi da al'adunsu ɗungurungum ba.

''Har yanzu muna gudanar da wasu al'adunmu na gargajiya; yanzu wannan gari da kake gani na Ile-Ife sun yi amanna cewa daga can ne hasken duniya yake fitowa.

In suna bikinsu na al'ada za ka ga sun ɗauko wani mayafi fari ko harami su yafa, amma ba saboda addini ba sai domin tsafe-tsafe da sauran al'adunsu.

Hakanan idan ana so a tsinewa mutum ana yi masa barazana da cewa za a fada wa Oduduwa ya la'ance shi- kamar ga Bayerabe domin mutum ya kiyaye.

Idan Oduduwa ya tsine maka tsinuwar za ta tabbata. To amma har yanzu akwai sauran al'adun namu sai dai ba su da karfi- sakamakon shigowar addinin Musulunci da kuma Kiristanci da kuma shigowar bakin al'adu na

Al’adun Mutuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Abinda ya shafi kide-kide da rawa na Yarbawa har kwanan gobe ana yi ba a bar su ba. Waɗannan ba a fitar da su daga cikin al'adu ba.

Yanzu misali a abinda ya shafi mutuwa a jihohin Ekiti da Ondo a kan ajiye gawa domin a yi mata biki- to amma kamar anan Osun musamman a yankunan da Musulunci ya yi ƙarfi, ba mu yarda da wannan al'ada ba.''

Ita kuwa wannan malama mai suna Mrs. Busola ta ce al'adunsu da suka shafi abinci da sauransu suna cikin abubuwan da suke alfahari da aka haifesu cikin ƙabilar Yarbawa.

''Yarbawa mutane ne da ke biyayya ga manyansu da marabtar baƙi da kuma nuna kulawa ga jama'a. Muna mu'amala da wasu ƙabilu da kuma mabiya addinai daban-daban.

''Addininmu na gargajiya suna nuna allolinmu na baiwa kamar Ogun da Sango da Osun da Obatalamo da sauransu. Eh! Ina godiya ga Oludumare da ya halicce ni Bayarbiya.

''Matanmu suna sanya tufafin Iro da buba tare da gele, yayin da mazajenmu kan sanya kayan saki kamar hula da buba da shokoto.

''Ni Bayarbiya ce, kuma ina alfahari da al'adata. Al'adun Yarbawa suna da ban sha'awa wadanda suke nuna asalinmu wanda shi ne garin Ile-Ife.

''Kuma abincinmu kamar Iyo da dakakkiyar sakwara da Amala da Eba waɗanda ake yin su da rogo suna kwadaita min cinsu da samun nishadi,'' in ji Mrs Busola.

Wasu al'adu da wannan ƙabila ta yi fice a kansu sun haɗa da doba'le da akan yi ruf da ciki a fadi a gaban sarki domin yin gaisuwa a gaban sarki; a yayin da mata kuwa kan tsaya bisa gwiwowinsu a kasa sa'annan su gaishe da Basarake.

Abincin Yarbawa

[gyara sashe | gyara masomin]

A kasar Yarbawa ma dai ana samun Oloyes kwatankwacin fadawan sarki da ake samu a masarautun da ke arewacin Naijeriya. Abincin da aka fi saninsu da shi dai sun hada teba da suke kira E'ba da doya da kuma .

Yarbawa suna noma kan wadannan cimaka, sai dai mafi yawa su ne 'ya'yan itace- kuma akwai mafarauta a cikinsu.

A baya ana samun magidanci na aurarraki da yawa, sai dai kuma abinda addini ya zo da shi da kuma zuwan Turawan mulkin mallka a sannu-sannu an yi watsi da wasu daga cikinsu.

Game da haihuwa kuwa duk yaron da yake shi ne dan fari akan kirashi da Dawodu a yayin da 'ya mace ake kira ta da Bee're.

Kaɗe-kaɗen Yarbawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Kaɗe-kaɗe da kuma imani da magungunan gargajiya har kwanan gobe suna yin tasiri cikin rayuwarsu. Malam AbdulKabir wanda Bayerabe ne ya gasgata fifita al'ada a wannan shiyya.

Yara daga wannan ƙabila dai ana ba su tarihin Oduduwa, wani mahaluki ne cikakken jarumi da ya gagari maza da dauloli. Wanda da haka ake cusawa yara koyon al'adu da tsayawa a kansu.

Malam Abdulkabir ya ce sun san da haka a lokacin da suke ƙanana.

Guraren Zama

[gyara sashe | gyara masomin]
nayi gyara nasa photo

Ana samu Yarabawa a ƙasashen duniya da dama daga ciki akwai Najeriya inda nan ce ƙasarsu ta gado; dukkanin Yankin Yammacin Najeriya nasu ne, kuma suna da cikakkun jahohi guda shida (Lagos, Ogun, Ondo, Oyo, Osun da kuma Ekiti), Kwara ma da ke Arewacin Najeriya da kuma wani yanki na jahar Kogi duk suna cikin Ƙasar Yaraba. Haka nan kuma ana samun Yarabawa a ƙasashe irin su Jamhuriyar Benin (Benin Republic); Togo; Kudancin Amurka (South America); Yammacin Indiya (West Indies); Cuba (Onadeko, 2008). Barazil da kuma Salo.

Ogunbado (2003) ya ƙara da ƙasashe irin su Ivory Coast, Ghana, Latin Amurka kamar a Trinidad da Tobago, sannan kuma bai gushe ba yana mai cewa ana samun Yarabawa har a cikin Amurka, akwai ma wani ƙauye da ake kira Oyotuni wanda yake a kusa da Sheldon, Beaufort a Kudancin Carolina, wanda sunansa ya samo asali ne daga Oyo ta Najeriya.

Wannan mutum dai shi ne Bayarabe a taƙaice. Sauran Abubuwan da suka shafe rayuwarsa kuma, kamar abin da ya shafi Ƙasa, al’adu, addini, zamantakewa da haɗuwarsu da wasu mutanen kamar zuwan Hausawa da sauransu, kowane an yi bayaninsa a muhallin da ya dace. Ziyarci sauran majonan da ke haɗe da wannan shafin domin jin yadda akabhaihu a ragaya.