Yawon Buɗe Ido a Nijar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yawon Buɗe Ido a Nijar
tourism in a region (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara Yawon bude ido
Ƙasa Nijar
waniyankin a nijer

Akwai karancin yawon bude ido a Nijar. Yawancin masana'antar yawon buɗe ido na arewacin kasar, inda birnin Agadez ke ba da damar shiga hamada/sahara. [1] Sauran wuraren da ake ganin yawon bude ido su ne babban birnin kasar, Yamai, yankunan da ke kusa da kogin Neja, da kuma wuraren ajiya irin su Kouré [1] wanda aka sani da giraffes na yammacin Afirka.[2]

Yawon buɗe ido a Arewacin Nijar ya fara bunkasa a shekarun 1970s. Yawon bude ya ragu a lokacin tawayen Abzinawa a farkon 90s. [1]

Akwai ci gaba da gargadin balaguro zuwa Nijar saboda ta'addanci sakamakon tashin hankalin Magrib (2002-yanzu) da kuma ta'addancin Boko Haram.[3] Hare-haren Toumour na shekarar 2020 ya faru ne a ranar 12 ga watan Disamba, 2020, lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari kauyen Toumour, inda suka kashe mutane 28 tare da raunata kusan mutane 100.[4] [ana buƙatar hujja]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 Geels, Jolijn (2006). Niger: The Bradt Travel Guide . Bradt Travel Guides . p. 41. ISBN 978-1-84162-152-4Empty citation (help)
  2. https://www.worlddata.info/africa/niger/tourism.php
  3. https://fortuneofafrica.com/niger/tourism-in-niger/
  4. https://www.tripadvisor.com/Tourism-g293823-Niamey-Vacations.html