Zulai Bebeji
Zulai Bebeji jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ta jima a masana'antar an damawa da ita. Tana Bada gudummawa tana taka rawa a matsayin uwa a masana'antar ta kara yin suna ne data fito a fim Mai dogon zango Mai suna "KISHIYA TACE" Wanda suke da jarumi Lawan Ahmad , Maryam Malika, Samha M Inuwa.[1]
Taƙaitaccen Tarihin Ta
[gyara sashe | gyara masomin]Cikakken sunan ta shine Zulaihat Abdullahi Aliyu Bebeji.[2] An haife ta a Karamar hukumar Bebeji dake Jihar Kano. Ta girma a Gawuna Karamar hukumar Nasarawa a hannun yayar mahaifiyar ta Mai suna hajiya lariya da mijin ta mlm ladan, Ta fara karatun Boko Dana islama ne a gawuna daga baya tai aure bayan tayi aure ta cigaba da karatu . Daga Nan ta fito a masana'antar fim inda tayi shekaru da yawa a[3] masana'antar . Iyayenta sun rasu gaba daya. Da tayi aure ta haifi Yara shida daga baya biyu suka rasu yanzun tana da Yara hudu Kenan da jikoki da dama[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://m.youtube.com/watch?v=q6jUwsT-yxo
- ↑ https://www.asuadailypost.com.ng/2023/02/takaitaccen-tarihin-hajiya-zulai-bebeji.html?m=1
- ↑ https://www.blueprint.ng/i-dont-have-any-mentor-in-kannywood-zulai-bebeji/
- ↑ https://fimmagazine.com/sukar-da-aka-ri%C6%99a-yi-wa-yan-zaman-shahada-ce-aka-kwaso-aka-ya%C9%93a-wa-yan-kannywood-zulai-bebeji/