Lawan Ahmad
Lawan Ahmad | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bakori, 1982 (41/42 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Yusuf Maitama Sule Un AUWALI SANI BENA (en) |
Harsuna |
Turanci Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo |
Lawan Ahmad ya kasance dan wasan fim din Najeriya ne,[1] jarumi ne kuma mai shirya fina-finan daracta kuma producer[2] a masana'antar shirya fina-finan Kannywood. Ya fito ne daga "FKD FILM PRODUCTION", ya shigo cikin harkar fim ta hanyar gudummawar Ahmad Suhu. [3]
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Lawan Yahaya Ahmad a Bakori (LGA) da ke a jihar Katsina a ranar 13 ga watan Maris shekara ta alif dari tara da tamanin da biyu 1982. Ya halarci makarantar firamarensa a "Nadabo Primary School Bakori" daga shekara ta alif dari tara da tamanin da bakwai 1987 zuwa shekara ta alif dari tara da casa'in da uku 1993. Ya gama karamar sakandirensa a "Government Day Secondary School Bakori, kuma a karshe ya kammala Babbar Sakandare (SSCE) a "Government Day Secondary School Sharada"daga shekara ta 1994 zuwa shekara ta 2000.
Ya cigaba da karatunsa a "Federal College Of Education Kano daga shekara ta 2002 zuwa shekara ta 2004. Lawan Ahmad ya halarci jami'ar " Yusif Maitama Sule University Kano " daga shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2017.
Jarumin ya shiga masana'antar fina -finai ta Kannywood a cikin shekara ta 1999 kuma ya fara fitowa a fim din [SIRADI] wanda ya zama fim dinsa na farko.
Filmography da aka zaɓa
[gyara sashe | gyara masomin]- Zuma
- Sharhi
- Bakace
- Kolo
- Taraliya
- Sansani
- Sai wata rana
- Wasila 2010
- Haske
- Kalamu wahid
- Siradi
- Maya
- Muradin Kaina
- Ni da kai da shi
- Shanya
- Bani ba ke
- Abun da kayi
- Hauwa kulu
Lambobin yabo
[gyara sashe | gyara masomin]- Mafi Kyawun Sabon Comer a fim "ZUMA" daga MTN Awards a 2004
- Fitaccen dan wasa mai tallafi a cikin fim "DA'IMAN" na MTN Awards a shekarar 2016
- Fitaccen jarumin da ya shahara da "Kyautar gwarzon Katsina a shekarar 2017
- Mafi kyawun Jarumi a fim DA'IMAN ta "City People Awards" a cikin 2018
- Fitaccen dan wasa da "AFRO HOLLYWOOD AWARDS LONDON " a cikin Fim "ZAN RAYU DAKE" a cikin 2019
- Mafi Kyawun 'Yan wasa a cikin fim din "Zan Rayu Dake" na Amma Awards Season 5 in 2019.
- Mafi kyawu da birgewa a cikin fim (series film) din "IZZAR SO" tun daga 2020 har zuwa yanzu.
Nasara
[gyara sashe | gyara masomin]Lawan Ahmad shi ne Shugaba / GASKIYA na "BAKORI ENTERTAINMENT " dandamalin da ke kwarewa wajen yin fim, samar da abubuwan da ke ciki, da kuma kafofin watsa labarai. Ya shirya fina-finan Haus<<a da yawa kamar: [Ana bukatan hujja][4]
- Shanya
- Bani Bake
- Kolo
- Sadaukarwa
- Abun da ka yi
- Dashen haka
- Koni ko ke
- Izzar so (Series Film)
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Onuzulike, Uchenna, 1971- (2008). Nollywood video film : Nigerian movies as indigenous voice. VDM Verlap Dr. Müller. ISBN 978-3-639-13564-0. OCLC 678098062.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
- ↑ Victoria, Bamas (2018-10-26). "Kannywood's Lawan Ahmed marks 10th wedding anniversary". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2020-09-20.
- ↑ "INTERVIEW: Why I'm the best Kannywood actor – Lawal Ahmad | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2016-04-02. Retrieved 2020-09-20.
- ↑ www.bbc hausa.org.com