Ƙuli-ƙuli
| Ƙuli-ƙuli | |
|---|---|
|
| |
| Kayan haɗi | gyaɗa |
| Kayan haɗi |
Gyaɗa, seasoning (en) |
| Tarihi | |
| Asali | Najeriya |
Ƙuli-ƙuli (Groundnut cake) Kalmar ƙuli-ƙuli dai kalma ce da take a cikin harshen Hausa. Wani abin ci ne da ake yin amfani da shi a matsayin mahaɗi. Haka zalika ƙuli-ƙuli ana iya cinsa ta hanyoyi da dama wasu sukan sanya shi a cikin garin rogo su sha, wasu kuma suna cinsa da Mazanƙwaila, wasu kuma suna cin sa haka nan zallansa.[1] Abinci ne na mutanen yammacin Afrika wanda ake samar da shi daga gyada. Sanannen abinci ne a ƙasashen Afrika irin su Najeriya, Benin, Arewacin Kamaru da Ghana. Ana iya cin sa shi kaɗai. Ana kuma cin shi a Koko, fura, kamu, kuma wani lokacin ana yin kwaɗo da shi. Kuma ana haɗa shi wajen yin Tsire da Kilishi.[1][2].
Yadda ake haɗa Ƙuli-ƙuli
[gyara sashe | gyara masomin]
Da farko ana samun Gyaɗa bayan an ɓare ta sai a soya ta sannan a murje ta a fece wato a hure dukan bawon gyadar. Daganan kuma sai a markaɗa ta. Bayan an markaɗa ta ne sai kuma za'ayi amfani da Turmi a yi ta juya ta ana juyata har sai manta duka an gama matse shi, ita kuma gyaɗar ta koma Tunkuza. Wannan tunkuzar za'a dauka a sarrafa ta zuwa irin yadda ake buƙatar ta kamar gutsure-gutsure ko a taɓe. Daga nan sai ɗora Man gyaɗar da aka matse daga tunkuzar a kasko sai a hura wuta, idan man ya ɗau zafi sosai, sai a rinƙa zuba curi-curi ko taɓaɓɓiyar tunkuzar cikin man ana soyawa anayi ana ɗan juyawa kaɗan-kaɗan. Bayan ya gama soyuwa to shikenan Ƙuli-ƙuli ya kammalu.[3]

Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]- Gyaɗa da ake sarrafawa ayi Kuli-Kuli
- Wata mai soya Kuli-Kuli
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-11-30. Retrieved 2020-12-27.
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
- ↑ Ibrahim, Salisu (21 November 2021). "Mu leƙa madafa: Dalla-dalla yadda ake hada wani nau'in Kuli-Kuli mai ban sha'awa". Legit.hausa.ng. Retrieved 22 November 2021.