Jump to content

Ƙungiyar Gyaɗa ta Afirka

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ƙungiyar gyaɗa ta Afirka ƙungiya ce ta Gwamnati da aka tsara don inganta gyaɗa da aka samar a kasashen Gambiya, Mali, Nijar, Senegal, Sudan da Najeriya.

An kafa ta a watan Yunin 1964, AGC ta kasance a Legas, Najeriya, daga lokacin da aka kafa ta har zuwa 2005, lokacin da ta koma Kano.. Ta koma a shekara ta 2005 saboda maganganu da kungiyar manoma ta Groundnut ta Najeriya ta yi. Babban sakataren kungiyar na farko shi ne Jacques Diouf .

An Samar da AGC ne don inganta hadin gwiwar tattalin arziki da tattauna gama garin matsalolin da aka saba da su kamar farashin kayayyaki tsakanin manyan masu samar da kayan masarufi na africa, yana kuma aiki a matsayin tallace-tallace na yau da kullum, bincike da kuma tallan tsari ga en gongiyar.[1] Gwamnatocin kasashe masu samarwa a lokacin samun 'yancin kai sun sami kashi mai yawa na kudaden shiga na kasa da kudaden musaya na kasashen waje daga groundnut. An fara AGC ne don taimakawa wajen kafa aikin hadin gwiwa don daidaita farashi da ci gaba da sha'awar masu samarwa a kasuwannin kayayyaki na duniya.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Groundnut Producers' Lagos Meeting. The Financial Times (London, England),Wednesday, June 29, 1966; pg. 2

Haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]