Adaobi Tricia Nwaubani
Adaobi Tricia Nwaubani | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Enugu, 1976 (47/48 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Mazauni | Jaguar Abuja |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Ibadan Digiri Kwalejin 'yan mata ta Gwamnatin Tarayya, Owerri |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Marubuci, marubuci da ɗan jarida |
Muhimman ayyuka |
I Do Not Come To You By Chance (en) Buried Beneath the Baobab Tree (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Adaobi Tricia Obinne Nwaubani ƴar Najeriya, marubuciyar littattafai, insha'i ce kuma 'yar jarida wacce aka haifa a shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da shida 1976.[1] Littafinta na farko, I Do Not Come To You By Chance,[2] ta lashe lambobin yabo ta Marubutan Commonwealth ta alif dubu biyu da goma 2010 a matsayin Littafin Na Farko na musamman (a Afirka),[3][4] Lambar yabo ta Betty Trask First Book,[5] kuma jaridar Washington Post ta jero ta matsayin daya daga Littattafai Musamman na shekarar if dubu biyu da tara 2009.[6] Llittafinta na farko akan labarin Matasa, Buried Beneath the Baobab Tree, dangane da hirar da aka yi da 'yan matan da kungiyar Boko Haram suka sace wanda kamfanin HarperCollins ta wallafa acikin watan Satumbar shekarar alif dubu biyu da goma sha takwas
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Nwaubani wacce aka haifa a Enugu, Najeriya, ya Chif Chukwuma Hope Nwaubani da Patricia Uberife Nwaubani a shekara ta alif dubu daya da dari tara da saba'in da shida 1976, iyayenta biyu sun tashi ne a garinsu na Umuahia, a Jihar Abia, a tsakanin kabilar Ibo. Iyalinta sun fito ne daga mambobin tsarin masarautar Najeriya; kakanta Chief Nwaubani Ogogo Oriaku - asalin sunan da aka rada mai - ya kasance shahararren bawan kamfanin Royal Niger Company a karni na goma sha tara 19.
Tana da shekara goma 10, ta bar gida don shiga makarantar allo a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Mata da ke Owerri. Ta yi karatun Psychologyat ne a jami’ar Ibadan, babbar jami’ar Nijeriya. Lokacin da take budurwa, Nwaubani a asirce ta yi burin zama wakiliyar CIA ko KGB. Ta samu kudin shiga na farko ne daga lashe gasar rubutu tun tana 'yar shekara goma sha ukku 13. Mahaifiyarta kami ce ga Flora Nwapa, marubuciya itace mace ta farko a Afirka da ta fara bugawa. littafi. A shekarunta na farko a Jami'a, ta kasance mamba a kungiyar Idia Hall Chess, sannan kuma memba ce a kungiyar mawaka ta jami'ar.
Nwaubani na daya daga cikin manyan ma'aikatan editocin fitattun jaridun NEXTnewspapers na Najeriya, wanda dan jaridar da ya ci kyautar Pulitzer Dele Olojede ya kafa.
Ba Na Zuwa Gare ku Ba, Hasalima ita ce littafin Nwaubani na farko, wanda aka buga a shekarar alif 2009. Littafin ya bayyana ne a duniyar zambar imel na Najeriya, littafin ya ba da labarin wani saurayi, Kingsley, wanda ya koma ga Kawunsa Boniface don neman belin danginsa daga talauci. A cikin shekarar alif dubu biyu da goma sha tara 2019,
Adaobi Tricia Nwaubani na zaune ne a Abuja, Najeriya, inda take aiki a matsayin mai ba da shawara
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Adaobi Tricia Nwaubani". All African Books. Retrieved 26 August 2022.
- ↑ Nwaubani, Adaobi Tricia (2009). I Do Not Come to You by Chance. Hachette UK. ISBN 9780297858720.
- ↑ "Marié Heese and Adaobi Tricia Nwaubani Win the 2010 Commonwealth Writers Prize – Africa Region Awards". 11 March 2010. Retrieved 14 June 2013.
- ↑ Nwaubani, Adaobi Tricia (7 October 2012). "My degree is better than yours". Premium Times. Retrieved 14 June 2013.
- ↑ "The Betty Trask Prizes and Awards". The Society of Authors. Archived from the original on 22 July 2011. Retrieved 14 June 2013.
- ↑ "Best Books of 2009". Washington Post.