Aduwaa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
bishiyar aduwa da furenta
Aduwaa
Conservation status

Least Concern (en) Fassara  (IUCN 3.1)
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderZygophyllales (en) Zygophyllales
DangiZygophyllaceae (en) Zygophyllaceae
GenusBalanites (en) Balanites
jinsi Balanites aegyptiaca
Delile, 1813
bishiyar Aduwa da ƴaƴanta ɗanyu

Aduwa tana daga cikin nau'in ita ce wato bishiyoyi sai dai kuma ita tana daga bishiyoyi masu 'ƴa'ƴa kuma ana amfani da 'ƴa' ƴanta ta fannoni daban-daban. Ana tsotsan 'ƴa'ƴanta ana kuma anfani da man aduwa. An fi samun bishiyar aduwa a ƙasashen Afirka sai kuma wani ɓangare na yankin Asiya, a taƙaice an fi samun bishiyar aduwa a Sahara saboda haka ne ma turawa ke kiranta da Turanci da "Desert date" sai kuma akan same ta a wasu yankunan ƙasar indiya a yankin Rajastan (Rajasthan), Gujarat, Dekan (Deccan) da kuma Madiya Pradesh. Sai dai kuma ƙasar Sanegal ita ce ta fi kowace ƙasa bishiyar aduwa duba da bishiyar aduwa kusan ko'ina ana samunta a Senagal Tama fi sauran bishiyoyin yawa a ƙasar. Haka ana kiran ta da Turanci da (soap berry tree) ko kuma (thorn tree). [1][2][3][4][5][6]

ƙwallon ƴaƴan Aduwa

Siffan bishiyar aduwa[gyara sashe | gyara masomin]

Haka bishiyar aduwa tana tsawo sosai sai kuma 'ƴa'ƴanta kafin su bura ko kuma su nuna kore ne shar, idan kuma sun nuna sai su koma ruwan gwaiduwan kwai wato yalo (yellow). Sai kuma ɗan-ɗanonta tsami-tsami da ɗaci-ɗaci 'ƴa' ƴanta na da sauƙi wajen tsotsansu, haka aduwa tana da ƙwallo bayan an gama tsotsa ƙwallon ta yanada tauri sosai. Ganyen ƙanana ne bishiyar aduwa tana yin ganye sosai a yayin da ta kai shekaru biyar zuwa bakwai (5-7 years) haka tana fara ƴaƴa daga shekara goma zuwa sha biyar (10-15) sai kuma tana yin ƴaƴa masu yawa daga shekara ishirin zuwa ishirin da biyar (20-25).

Amfanin ƴa'ƴan aduwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ƴaƴan aduwa suna da amfani sosai ga jikin Ɗan Adam ga wasu daga magungunan da takeyi:

 • Aduwa tana maganin Asma
 • Aduwa tana maganin shawara
 • Tana sauƙaƙa cutar Farfaɗiya
 • Man aduwa na kawar da kumburi
 • Yana kawar da ciwon bugawar zuciya
 • Aduwa tana maganin fitsarin jini
 • Aduwa na maganin tsutsar ciki
 • Aduwa tana maganin sanyin ƙashi
 • Aduwa takan tsayar da zawo da amai idan aka tsotsa ƴaƴanta.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. Usman, Jamil (21 December 2019). "Amfani 12 da aduwa ke yi a jikin dan adam". legit hausa. Retrieved 10 August 2021.
 2. Shu'aibu, Yusuf (6 July 2018). "Amfanin Aduwa Ga Lafiyar Dan'adam". Retrieved 10 August 2021.
 3. "Africa - Desert Date". Clarin.
 4. "Balanites aegyptiaca". Tropical.theferns. Archived from the original on 2021-08-10. Retrieved 2021-08-10.
 5. "Amfanin Icce Da Yayan Aduwa Ajikin Mutane". YouTube.
 6. Abdullahi, Aliyu (2 May 2016). "Amfanin 'ya'yan itatuwan gargajiyar Hausa ga lafiyar jikin dan Adam". dw.hausa. Retrieved 10 August 2021.