Ahmed Sani Stores
![]() | |||
---|---|---|---|
Mayu 2011 - Mayu 2015 ← Ibrahim M. Ida - Kurfi Umaru → District: Katsina Central | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Katsina, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Congress for Progressive Change (en) ![]() |
Ahmed Sani Stores ɗan siyasar Najeriya ne wanda aka zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya, a jihar Katsina, a zaɓen kasa na ranar 9 ga Afrilu 2011. An zaɓe shi a tikitin jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC).
Farkon rayuwa da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Ahmed Sani Stores a unguwar Kangiwa da ke cikin birnin Katsina. Ya yi karatu a North East Worcestershire College, Bromsgrove, London, kuma ya zama mai ba da shawara kan kuɗi da fitarwa.
Ayyuka da Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]
Yana da gogewa a fannin samar da wutar lantarki ta hasken rana da iska.[1] Yayin da yake zaune a Landan, a shekarar 2003 yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa gidauniyar kyakkyawan shugabanci da ci gaba a Najeriya.[2]
Ahmed ya dawo Najeriya domin fafatawa a zaɓen Sanata.[2] An bayyana cewa, a wani lokaci a lokacin yakin neman zaɓen an kai Ahmed Sani Stores zuwa kotun majistare inda aka tuhume shi da aikata ta’addanci.[3]
A zaɓen da aka yi a ranar 9 ga Afrilun 2011, Ahmed Sani Store ya doke Ibrahim M. Ida na jam'iyyar PDP da kuri'u 267,154, inda wanda aka kayar ya samu 188,205.[4]
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "Four parties fight for Katsina's three seats". The Nigerian Daily. April 5, 2011. Archived from the original on 2012-03-23. Retrieved 2011-04-25.
- ↑ 2.0 2.1 "I'm in politics to solve my people's problems". National Mirror. 2011-02-12. Archived from the original on 2012-03-20. Retrieved 2011-04-25.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ Hussain J. Ibrahim; Solomon Chung; Hir Joseph (26 March 2011). "Political parties under attack from each other". Archived from the original on 2 September 2011. Retrieved 2011-04-25.
- ↑ John Abayomi (April 10, 2011). "NASS Election :Yar'Adua's daughter loses in Katsina". Vanguard. Retrieved 2011-04-25.