Jump to content

Aisha Lemu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aisha Lemu
Rayuwa
Cikakken suna Bridget Aisha Honey
Haihuwa Poole (en) Fassara, 1940
ƙasa Birtaniya
Mutuwa Minna, 5 ga Janairu, 2019
Ƴan uwa
Abokiyar zama Ahmed Lemu
Karatu
Makaranta School of Oriental and African Studies, University of London (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a marubuci
Imani
Addini Musulunci

Aisha Bridget Lemu Shahararriyar marubuciyar litattafan addinin Musulunci ce haifaffiyar Birtaniya Kuma mazauniyar birnin Minna a tarayyar Najeriya.

An haifi marigayiya Bridget Aisha a garin Poole na yankin Dorset na ƙasar Ingila a shekara ta 1940. Kumar ta karɓi addinin Musulunci a shekara ta 1961, ta rasu a garin minna na jahar Neja ranar 5 ga Janairu na shekara ta 2019.

Tana da shekara 13 da haihuwa sai ta fara tunanin sauya addininta, inda ta fara da duba addinan Hindu da na Bhudda amma basu gamsar da ita ba.

Ta yi karatun jami'a a makarantar koyon al'adu da harsunan ƙasar Sin da na Afirka a jam'iar Landan (SOAS), inda ta karanta tarihi da al'adu da kuma harshen kasar Sin.

A jami'ar ne kuma ta fara haduwa da dalibai Musulmai waɗanda suka riƙa ba ta litattafan addinin Musulunci, kuma ba da daewa ba sai ta musulunta a shekara ta 1961, a lokacin tana shekararta ta farko a jami'a. A lokacin ne ta bayar da gudunmawarta wajen kafa kungiyar dalibai Musulmai na makarantar ta SOAS a jami'ar Landan, kuma ita ce sakatariyar ƙungiyar ta farko.

Bayan ta kammala karatun digiri na farko a jami'ar Landan, sai Aisha Lemu ta koma domin karatun babban digiri a kan harshen Ingilishi, kuma a lokacin ne ta fara ganin Sheikh Ahmed Lemu, wanda shi kuma ya isa Landan ne domin karo ilimi a jam'iar ta Landan.

Bayan kammala digirinta na biyu sai ta koma Kano a shekara ta 1966, inda ta fara koyarwa a makarantar nazarin Larabci, a lokacin shi Sheikh Ahmed Lemu ke shugabancin makarantar. Ta tafi Sokoto domin kama aiki a matsayin shugabar makarantar mata ta gwamnati.

Daga baya ta koma jihar Neja bayan da aka kirkiri jihar daga cikin jihar Arewa maso yamma ta da a shekara ta 1976, kuma ta zama shugabar makarantar horar da malamai mata ta Minna har 1978.

Ita da maigidanta sun kafa Gidauniyar Ilimin Islama (IET), kuma ta kafa babbar ƙungiyar mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) a shekara ta 1985.

An ɗaura mata aure da Ahmed Lemu a watan Afrilun shekara ta 1968, inda Aisha ta kasance matarsa ta biyu.

Litattafanta

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta rasu a garin minna na jahar Neja ranar 5 ga watan janairun, shekara ta 2019.