Akshata Murty

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Akshata Murty
ɗan kasuwa


babban mai gudanarwa

Rayuwa
Haihuwa Hubballi (en) Fassara, ga Afirilu, 1980 (43/44 shekaru)
ƙasa Indiya
Ƴan uwa
Mahaifi N. R. Narayana Murthy
Mahaifiya Sudha Murthy
Abokiyar zama Rishi Sunak  (30 ga Augusta, 2009 -
Ahali Rohan Murthy (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Makaranta Baldwin Girls High School (en) Fassara 1998)
Fashion Institute of Design & Merchandising (en) Fassara
Claremont McKenna College (en) Fassara
(1998 - 2002) : ikonomi, Faransanci
Jami'ar Stanford
(2004 - 2006) Master of Business Administration (en) Fassara
Matakin karatu Master of Business Administration (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Turanci
Harshen Hindu
Kannada
Sana'a
Sana'a Mai tsara tufafi da manager (en) Fassara
Employers Infosys (en) Fassara
Jamie Oliver (en) Fassara
Wendy's (en) Fassara
Imani
Addini Hinduism (en) Fassara
IMDb nm13641361

Akshata Narayan Murty (an haifeta a watan Afrilu a 1980) magajiya ce 'yar kasar Indiya, 'yar kasuwa, mai kawata kaya kuma 'yar jari hujja ce. Tana auren Rishi Sunak, firaministan Ingila kuma shugaban jam'iyyar Conservative. A cewar jaridar Sunday Times Rich Lis, Murty da Sunak su ne 222 a jerin masu kudi a Birtaniya a shekarar 2022, suna da jimillar dukiya fam miliyan 730 wanda yayi daidai da dala miliyan 830.[1] [2] Ita diyar N. R. Narayana Murty, wanda ya kirkiro kamfanin Infosys da kuma Sudha Murty. Tana kashi 0.93 na hannun jari a kamfanin Infosys tare kuma da wasu hannayen jari a wasu kamfanonin kasuwanci na kasar Birtaniya.[3] [4] [5]

Tarihi da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

An haife Akshata Murty a watan Afrilu a shekarar 1980 a Hubil dake a kasar Indiya, [6] [7] kakanninta na bangaren uwa suka reneta, lokacin mahaifinta N. R. Narayana Murty da mahaifiyarta Sudha Murty suna aikin kafa kamfanin fasaha na Infosys.[8] [9] Mahifiyarta itace mace ta farko injiniya da tayi ma kamfanin TATA Engineering da Locomotive a lokacin shine babban kamfanin kera mota na kasar Indiya, daga bisani ta zama mai taimakon mutane.[10] Murty nada dan uwa guda daya, Rohan Murty, [11] sun girma a Jayanagar ne wanda yake a wajen garin Bangalore.[12] A shekarun 1990, [13] Murty tayi karatu a babbar makarantar mata Baldwin dake a Bangalore, a shekarar 1980 tayi karatun tattalin arziki da kuma harshen Faransanci a kwalejin Claremont McKenna dake Kalifoniya a dake kasar Amurka. [14] Tana da difloma a kan kera tafafi daga Fashion Institute of Design and Merchandising, [15] da kuma digiri na biyu a kan yadda ake kasuwanci daga jami'ar Stanford.[16]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]