Al-Bakara
Al-Bakara | |
---|---|
Surah | |
Bayanai | |
Bangare na | Al Kur'ani |
Suna a harshen gida | البقرة |
Suna a Kana | めうし |
Suna saboda | Saniya |
Akwai nau'insa ko fassara | 2. The Cow (en) da Q31204645 |
Harshen aiki ko suna | Larabci |
Full work available at URL (en) | quran.com… |
Has characteristic (en) | Saurin Medina |
Al-Bakara A(larabci| البقرة)A fassarar Hausa( Saniya) itace surah ta biyu kuma wacce take da mafi yawan ayoyi acikin Al-Qur'an.[1] Tana da yawan ayoyi guda 286, da kalmomi guda 6,201 da kuma yawan bakake guda 25,500.[2] Ita Surah Madaniyya, wato a garin Madina ne aka saukar da ita, bayan Hijira, banda wasu kadan daga cikin ayoyi daga ciki, wadanda aka saukar lokacin Hajjin Bankwana, wanda itace Hajjin Annabi Muhammad S.A.W.[3]
Itace surah mafi tsawo a Kur'ani. Itace Surah ta karshe da aka saukar a Madina, amma maban-bantan ayoyin an saukar dasu a wurare daban-daban, aya mai tsawo wanda take magana akan riba (cin kudin ruwa) kuma an saukar da ita ne a kusan karshen rayuwar Annabi Muhammad s.a.w, bayan bude garin Makkah (Maariful Quran).[4]
Aya ta 281, acikin surar itace aya ta karshe da aka saukar acikin Alkur'ani, a 10 ga watan Dhul al Hijjah shekara ta 10 A.H., sanda Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana kan gudanar da aikin Hajjin sa na karshe, kuma bayan kwanaki 80 zuwa 90 sai ya rasu. (Kurtubi).
Surah al-Bakarah ta wajabtar da yin azumi akan musulmi lokacin watan Ramadan.[5]
Anazarci
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Salwa M. S. El - Awa, Introduction to Textual Relations in Qur'an, pg. 1. Part of the Routledge Studies in the Qur'an series. London: Routledge, 2005. ISBN|9781134227471
- ↑ Ibn Kathir
- ↑ Mahmoud Ayoub, The Qurʾan and its interpreters, pg. 55. Albany: State University of New York Press, 1984. ISBN|9780791495469
- ↑ https://en.m.wikipedia.org/wiki/Ibn_Kathir#Tafsir
- ↑ Michael Binyon, Fighting is 'allowed' during the holy month of fasting The Times, 18 December 1998