Arwa bint Kurayz
Arwa bint Kurayz | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Makkah, unknown value |
Mutuwa | Madinah, unknown value |
Makwanci | Al-Baqi' |
Ƴan uwa | |
Mahaifiya | Umm Hakim bint Abdul Muttalib |
Abokiyar zama |
Affan ibn Abi al-'As (en) Uqba ibn Abi Mu'ayt (en) |
Yara |
view
|
Sana'a | |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Arwā bint Kurayz (Larabci: أَرْوَى بِنْت كُرَيْز) Ta kasance ce mahaifiyar Uthman ibn Affan, Sahabin Annabin Musulunci Muhammadu ne, kuma na uku daga cikin Rashidun ko "Khalifofi shiryayyu".[1]
Zuriyarsu
[gyara sashe | gyara masomin]Arwa ta kasance 'yar Kurayz ibn Rabi'ah ibn Habib ibn Abd Shams ibn Abd Manaf, don haka ta kasance daga Banu Abd-Shams, wani dangi na kabilar Quraysh.[2] Mahaifiyar Arwa ita ce Umm Hakim bint Abd al-Muttalib, don haka Arwa 'yar uwan Muhammadu ne.
Yara
[gyara sashe | gyara masomin]Arwa ta auri Affan ibn Abi al-'As kuma ta haifa masa Uthman da Amina. Bayan mutuwar Affan, Arwa ta auri Uqba ibn Abu Mu'ayt, wanda ta haifa masa al-Walid, 'Ammara, Khalid, Umm Kulthum, Umm Hakim da Hind.[3]
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Arwa bint Kurayz ta tuba zuwa addinin Musulunci kuma ta yi hijira zuwa Madina bayan 'yarta, Umm Kulthum bint Uqba. Ta ba da aminci ga Muhammadu, kuma ta kasance a Madina, har sai da ta mutu a lokacin Khalifancin ɗanta, Uthman ibn Affan . [3]
Dubi kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Adnan
- Family tree of Uthman