Jump to content

Babachir David Lawal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Babachir David Lawal
Secretary to the Government of the Federation (en) Fassara

27 ga Augusta, 2015 - 29 Oktoba 2017
Rayuwa
Haihuwa 2 Oktoba 1954 (70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Babachir David Lawal (An haifeshi ranar 2 ga watan Agustan shekarar alif ɗari tara da hamsin da hudu 1954)[1][2] a kauyen Kwambla da ke karamar hukumar Hong a jihar Adamawa. Ya kasance sakataren gwamnatin tarayya daga ranar 27 ga watan Agusta 215 zuwa 19 ga watan Afrilu, 2017[3]

Farkon rayuwa da Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

Yayi karatun firamare a St. Patrick's , Maiduguri a shekarar 1969 ya wuce Nigeria Military School Zaria, daga 1970 – 1974 domin yin karatunsa na sakandare . Daga nan ya halarci Makarantar Koyon Ilimi ta ABU Zariya, daga shekarar 1974 zuwa 1975. Lawal , ya karanci Injiniyan Lantarki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ya kammala a shekarar 1979 da Digiri na biyu (Electrical engineer) Daga baya ya samu digirin digirgir a shekarar 2007.[4]

Babachir ya fara aiki a kamfanin Delta Steel Company, Ovwian -Aladja inda ya kai matsayin Babban Injiniya , wannan ya kasance daga shekarar 1979 – 1984 . Daga nan ya yi aiki a Nigerian External Telecommunications Ltd, Lagos'a matsayin Babban Injiniya daga 1984 zuwa 1986. Ya kasance a Data Sciences Nigeria Ltd , daga 1986 zuwa 1989 , inda ya samu mukamin Manaja na Yanki , kafin ya tashi ya kafa kamfaninsa na Rholavision Engineering Ltd, Kaduna a shekarar 1990 .

Kafin ya kafa kamfanin sa na ICT da sadarwa a shekarar 1990.[5]

  • Memba a Nigeria Computer Society , NCS. Memba , Nigerian Society of Engineers, NSE, Memba a Majalisar Dokokin Injiniya a Najeriya , COREN. Memba , Cibiyar Gudanar da Ayyuka , PMI Memba, Cibiyar Nazarin Kasuwanci ta Duniya, IIBA Memba a Cibiyar Gudanarwa Canji, CMI
  • Mataimakin Kodineta na Jiha , The Buhari Campaign Organisation, Jihar Adamawa 2002- 2005.
  • State Coordinator ,The Buhari Campaign Organisation, Adamawa State , (2005 – 2010 )
  • Memba , Congress For Progressive Change Committee National Contact and Mobilization Committee (2010 - 2013)
  • Memba, Kwamitin Sabunta Canjin Cigaba na Majalisa, 2012
  • Memba, All Progressive Change Change Commite , 2013
  • Tsohon Babban Memba, Kwamitin Gudanarwa na Riko 2013 - 2014
  • Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa na arewa maso gabas 2014.
  • Memba, Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, 2015.[6]

Fagen siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Babachir ya shiga siyasa a shekarar 2002 ta hanyar zama mamba a jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP). ya rike ofisoshi da dama a jam'iyyar ANPP tun farko da kuma cikin tawagar yakin neman zaben Buhari ciki har da mataimakin Mai gudanarwa na kungiyar yakin neman zaben Buhari a jihar Adamawa.[7]

Shugaban Muhammadu Buhari ne ya naɗa shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya a shekarar 2015.[8] A ranar 30 ga Oktoban shekarar 2017, aka kore shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya bayan wani rahoto kan zargin sa da hannu wajen karkatar da kudaden agajin gaggawa.[9] Tare da maye gurbinsa da Boss Mustapha.

  1. https://www.bing.com/ck/a?!&&p=e2ccae057a518bcaJmltdHM9MTcxOTEwMDgwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTI2NQ&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Babachir+David+Lawal+biography&u=a1aHR0cHM6Ly9wZW9wbGVwaWxsLmNvbS9pL2JhYmFjaGlyLWRhdmlkLWxhd2FsLw&ntb=1https://www.bing.com/ck/a?!&&p=38388fedc8155155JmltdHM9MTcxOTEwMDgwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTIyMQ&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Babachir+David+Lawal+biography&u=a1aHR0cHM6Ly9jb250ZW50czEwMS5jb20vMjAyMC8wNC8xNC9iYWJhY2hpci1sYXdhbC1iaW9ncmFwaHktZWR1Y2F0aW9uLWNhcmVlci1hbmQtcGVyc29uYWwtbGlmZS8&ntb=1
  2. https://www.bing.com/ck/a?!&&p=6639f7c6aafcb690JmltdHM9MTcxOTEwMDgwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTI0Mw&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Babachir+David+Lawal+biography&u=a1aHR0cHM6Ly93d3cuY2VsZWJzYWdld2lraS5jb20vYmFiYWNoaXItZGF2aWQtbGF3YWw&ntb=1
  3. https://thenationonlineng.net/efcc-detains-ex-sgf-lawal-eight-hour-grilling/amp/<https://thenationonlineng.net/efcc-detains-ex-sgf-lawal-eight-hour-grilling/amp/
  4. https://www.africa-confidential.com/profile/id/3704/Babachir_Lawal
  5. http://saharareporters.com/2019/02/12/efcc-arraign-babachir-lawal-over-n544m-grass-cutting-scandal
  6. https://punchng.com/grass-cutting-scandal-court-adjourns-trial-of-babachir-lawal-five-others/
  7. https://www.thisdaylive.com/index.php/tag/babachir-david-lawal/[permanent dead link]
  8. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/189095-breaking-buhari-appoints-sgf-chief-of-staff-others.html
  9. https://www.google.com/amp/s/www.vanguardngr.com/2017/04/rise-fall-babachir-lawal/amp/