Babban Masallacin Yamai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Babban Masallacin Yamai
جامع نيامي الكبير
Wuri
JamhuriyaNijar
BirniNiamey
Coordinates 13°31′20″N 2°07′58″E / 13.5221°N 2.1329°E / 13.5221; 2.1329
Map
History and use
Opening1970s
Addini Musulunci
Contact
Address Boulevard Mali Béro, Niamey

Babban Masallacin Yamai (Faransanci: Grande mosquée de Niamey) masallaci ne na Islama da ke Yamai, Nijar. An gina shi a cikin 1970s.[1] Masallaci mafi girma a cikin gari, yana kusa da Islam Avenue. An yi ginin ne da kuɗi daga Libya. Yana fasalta wata minaret mai matakai 171 daga sama zuwa ƙasa.[2][3]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Masallacin ya kasance a cikin shekarun Alif 1970s, tare da cikakken goyon bayan Tallafin marigayi shugaban  kasar Libya Muhammad Gaddafi, ya gina masallacin mafi ban sha'awa, kuma mafi daraja a babban birnin [[Niamey|Niamy], Haske ne mai ƙyalli A jikin ginin masllacin, wanda kuma kyallin  ba me  lalacewa ba, bayan shekaru da yawa a ƙarƙashin Sahelian wato mutanan da suke rayuwa a Sahara cikin hasken rana da ƙura.  Kamar yadda ta mamaye fili mai fadi, yana daya daga cikin muhimman gine-ginen da ba  wata katanga mai tsayi ko shingen tsaro a jikin sa, A ranar Juma'a ita ce ranar da  yawan jama'a suke zuwa dan gudanar da Bautar Allah, da kuma lokacin karama/Babbar sallah da jama'ar yankin ke Haduwa da sauran mutane, Hakana kuma su ma wadanda ba musulmi ba, an yarda su shiga ciki suyi kallo har suyi hotuna aciki .  Akwai jagora a ciki me kula da mutane, mafi yawan lokuta, kuma ya kai ku don ganewa idanun ku abubuwan da aka kawata masallacin da su, Yana daya daga cikin mafi kyawun masallatai a Nijar, kuma me  tarihi.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Rosen, Armin (9 October 2015). "Niger's desert north is a glimpse into the destructive brilliance of Gaddafi's 42 years in power". Business Insider. Retrieved 10 July 2016.
  2. Sights in Niamey LonelyPlanet.com
  3. Niger: The Bradt Travel Guide on Google Books
  4. https://www.alluringworld.com/grand-mosque-of-niamey/