Balaraba Ramat Yakubu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Balaraba Ramat Yakubu
Juyin Sarauta Abuja.jpg
Rayuwa
Haihuwa Kano, 1959 (62/63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Yan'uwa
Siblings Murtala Mohammed
Karatu
Harsuna Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Marubuci/Marubuciya

Balaraba Ramat Yakubu kwarariyar marubuciyar littafan Hausa ne da ake wa lakabi littattafan soyayya. An haife ta a cikin birnin Kano a a shekarar 1959[1] . Tana daga kalilan marubuta da aka fassara littafinta zuwa harshen Inglishi. Rubuce - rubucenta sun fi bada muhimmanci akan zamantakewar aure da kuma gwagwarmayar mata a rayuwar Hausawa, musamman tauye hakkin mata da mazan Hausawa kan yi, zamu ga haka a littattafan ta kamar Budurwar zuciya da mashahurin littafin ta Alhaki kuikuyo ne.

Kuruciyarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Hajiya Balaraba kanwa ce ga tsohon shugaban kasar Nijeriya, marigayi Murtala Ramat Muhammed wanda aka yi wa juyin mulki a shekarar 1976.

Tun tana karama 'yar shekara 13 aka cire ta daga makaranta aka yi mata aure, wannan ne ma dalilin da ya sa take rubuce - rubucent da harshen Hausa maimakon turanci.[2]

Aiki[gyara sashe | Gyara masomin]

Budurwar Zuciya

Balaraba Ramat ta kasance mace tilo a cikin jagororin kungiyar marubuta mai suna  Raina Kama.[3]  Littafinta na farko shi ne  Budurwar Zuciya wanda aka wallafa a shekarar 1987. Daga nan ta ci gaba da rubuce - rubuce har zuwa daga bisani ta shiga harkar rubutun fim tare da shiryawa. A shekarar 1998, Muhammed Abdulkareem ya mayar da littafinta,  Alhaki Kwikwiyo Ne zuwa fim 1998.[4]

Har ila yau kuma, a shekarar 2012, wani kamfanin dab'i a kasar Indiya mai suna Blaft Publishers ya wallafa fassarar littafin Alhaki Kwikwiyo Ne zuwa Inglishi. Littafin ya samu kyakkyawan yabo [5][6]

An samar da wasu kyaututtuka ga matasan marubuta wanda aka rada wa kyautar sunan Balaraba Ramat Yakubu.[7]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Femke van Zeijl, "From illiterate child bride to famous Nigerian novelist", Al Jazeera (Features), 8 March 2016.
  2. "I write in Hausa 'cos I didn't get Western education - Says Murtala Muhammed's sister". NigeriaFilms.com. Retrieved 11 January 2013.
  3. Graham Furniss. "Hausa popular literature and video film: the rapid rise of cultural production in times of economic decline" (PDF). Retrieved 11 January 2013.
  4. Carmen Mccain (22 October 2012). "Hajiya Balaraba Ramat Yakubu's novel Alhaki Kuykuyo Ne/Sin is a Puppy Published in translation by Blaft". Retrieved 11 January 2013.
  5. Subashini Navaratnam (6 December 2012). "'Sin is a Puppy That Follows You Home', a Popular Hausa Novel, Is a Fast-Paced, Riveting Read". Retrieved 11 January 2013.
  6. Deepa Dharmadhikari. "Book Review: Full Hausa". Retrieved 11 January 2013.
  7. Awaal Gaata. "CATCHING THEM YOUNG: School gives prizes to students in Kano". Retrieved 11 January 2013.