Bilal Philip

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bilal Philip
Rayuwa
Haihuwa Kingston, Jamaica, 1947 (76/77 shekaru)
ƙasa Jamaika
Karatu
Makaranta King Saud University (en) Fassara
University of Wales (en) Fassara
Jarvis Collegiate Institute (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Malami da marubuci
Imani
Addini Salafiyya
bilalphilips.com

Abu Ameenah Bilal Philips, an haifeshi a kasar Jamaika a cikin shekara ta dubu daya da dari tara da arba'in da shida 1946Ac. Shi babban malamin musulunci ne a kasar Canada, sannan kuma marubuci ne na litattafan addinin musulunci da dama. Juma ma mallaki ne na jami'ar musulunci ta yanar gizo wato ISLAMIC ONLINE UNIVERSITY. Kuma yanzu haka yana zaune ne a kasar Qatar.[1] Yana baiyana a tashar talabijin ta Peace TV, mai watsa shirye-shiryenta awanniawanni ashirin da hudu (24-hours) a rana, da kuma tashar talabijin ta Islamic satellite TV channel.[2][3] Malam Philip ya ayyana kansa a matsayin dan Salafiya[4]

Tarihin rayuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

Hoton Bilal Philips.

Farkon inda ya tashi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi shehun malami Philips ne a garin Kingston, da ke a kasar Jamaica amma kuma ya taso ne a garin Toronto, da ke Ontario, a kasar Canada.[5]

Tarihin Ilimin sa[gyara sashe | gyara masomin]

Dr. Philips ya samu digirinsa ne na B.A a jami'ar Madina wato Islamic University of Medina sai kuma digirinsa na M.A. A fannin Aqidah daga jami'ar King Saud University a birnin Riyadh, na kasar Saudiyya. Sai kuma ya tafi jami'ar University of Wales, St. David's University College wacce a yanzu ake kira University of Wales, Trinity Saint David. Ya samu digirinsa na PhD. a shekarar 1993[6]

Kafa jami'ar Musulunci ta yanar gizo wato Islamic Online University[gyara sashe | gyara masomin]

Malam Philips ya kafa jami'ar musulunci ta yanar gizo ne a kasar Qatar kuma a yanzu haka Allah ya albarkaci jami'ar inda ta fadada sosai a sassan duniya.

Gwagwarmaya[gyara sashe | gyara masomin]

Kasar Birtaniya ta tuhumi Dr. Philips da laifin kutsa kai a wani harin ta'addanci[7]

Bilal Philip

Haka kuma Dr. Philips ya fito fili ya baiyanawa duniya tare da sukar masu ganin yin aure ga matan da basu kai munzali ba kamar fyade ne. Malam Philips ya yi kakkausar suka ga masu wannan ra'ayin hakan.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Gerard McManus. (2007-4-4). Radical sheik refused entry for Islamic talks. Herald Sun, retrieved December 13, 2007
  2. "Ofcom investigation into Peace TV | The Jewish Chronicle". Thejc.com. 2011-02-17. Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2016-06-05.
  3. "Archived copy". Archived from the original on April 2, 2015. Retrieved April 1, 2015. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)CS1 maint: archived copy as title (link)
  4. ""Controversial imam Bilal Philips says banning him won't stop his message"". The Globe and Mail. September 15, 2014. Retrieved 2016-06-05. If Salafi means that you’re a traditionalist that follows the scripture according to the early traditions, then yeah. I’m not a modernist. I’m not a person who makes his own individual interpretations according to the times
  5. Canadian imam Bilal Philips unwelcome in Philippines Ottawa Citizen
  6. "WorldCat library listing: Exorcism in Islam (Book, 1993) | University of Wales, Trinity St. David, Lampeter Campus". Archived from the original on 2018-03-14. Retrieved 2017-05-22.
  7. "Muslim Leaders Denounce Police Over Raids in Czech Capital". The New York Times. Retrieved 2016-06-05.