Bolaji Abdullahi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bolaji Abdullahi
Minister of Youth Development (en) Fassara

2011 - 2015
Akinlabi Olasunkanmi
Rayuwa
Haihuwa 1969 (54/55 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Lagos
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da ɗan jarida
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Bolaji Abdullahi (an haife shi a shekara ta 1969) ɗan siyasan Nijeriya ne kuma Marubuci daga Jihar Kwara . Ya yi aiki a majalisar ministocin tsohon Shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan a matsayin mai Girma Ministan Ci gaban Matasa a watan Yulin 2011 sannan daga baya ya zama Ministan Wasanni. Shine marubucin littafin "Sweet Sixteen" wanda JAMB / UTME 2019-2020 ya karba; Da Kuma littafin sa mai suna "Gold-How Jonathan won and lost Nigeria".

Farkon Rayuwa da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Abdullahi ya kammala digiri da mataki na biyu a fannin ilimin yaɗa labarai daga jami'ar Jihar Lagos a 2001.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1997, Abdullahi ya shiga aikin Jaridar ThisDay a matsayin mai kawo rahoto amma ya bar shekara guda zuwa Taron Shugabancin Afirka. Ya sake dawowa a 2002 inda ya zama Mataimakin Editan Jarida a 2003. Daga baya an nada shi a matsayin Mataimakin na Musamman, Sadarwa da Dabaru ga Gwamnan Jihar Kwara na lokacin, Dokta Bukola Saraki a 2003 sannan daga baya ya zama Mashawarci na Musamman kan Manufofi da Dabaru a 2005. Sannan an nada shi a matsayin Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Kwara daga 2007 zuwa 2011. Ya ci gaba da aiki a majalisar ministocin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan lokacin da aka nada shi a matsayin Mai Girma Ministan Ci gaban Matasa a watan Yulin 2011 sannan daga baya ya zama Ministan Wasanni.

A watan Disambar 2016, an sanar da Abdullahi a matsayin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC . A ranar 1 ga watan Agusta, 2018, a hukumance Abdullahi ya sauka daga mukamin sa na Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar All Progressives Congress ya kuma fice daga jam’iyyar.