Bruce Onobrakpeya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bruce Onobrakpeya
Rayuwa
Haihuwa Agbara-Otor, 30 ga Augusta, 1932 (91 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a painter (en) Fassara, Mai sassakawa da printmaker (en) Fassara
Employers Elizabeth City State University (en) Fassara
Kyaututtuka

Bruce Obomeyoma Onobrakpeya (an haife shi 30 ga watan Agusta shekara ta 1932) ɗan kasar Najeriya ne mai buga littattafai, da zane kuma mai sassaƙa. Ya baje kolinsa a garin Tate Modern a kasar London, National Museum of African Art of the Smithsonian Institute a garin Washington, DC da Malmö Konsthall a Malmö, Sweden. The National Gallery of Modern Art, Lagos yana da zane-zane masu ban sha'awa na Onobrakpeya kuma ana iya samun ayyukansa a gidan kayan tarihi na zamani na fasahar zamani na Najeriya, kodayake ba a nuna a watan Oktoba shekara ta 2017 [1].

Early years[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Bruce Onobrakpeya a garin Agbarha-Otor a jihar Delta, dan wani masassaƙa na Urhobo . Ya kuma girma a matsayin dan addinin Kiristanci, amma kuma ya koyi akidar gargajiya. Iyalansa sun koma garin Benin, dake Jihar Edo, tun yana yaro. Ya halarci makarantar sakandare ta Western Boys, inda Edward Ivehivboje ya koyar da shi kimiyya da fasaha, da kuma sauran darussa. Ya kuma halarci darussan zane dake British Council Art Club da ke birnin Benin. Onobrakpeya ya samu kwarin gwiwa tun daga zanen launi na Emmanuel Erabor . Bayan ya kammala karatu daga makarantar sakandare, Onobrakpeya ya ɗauki hayar malamin fasaha a Makarantar Sakandare ta Yamma wadda aka fi sani da Western Boys High School daga shekarar (1953–56). A shekarar 1956 ya tafi Jihar Ondo, inda ya koyar a Ondo Boys High School na tsawon shekara guda.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Bruce Onobrakpeya (Dedicated Exhibition)". ArtPortal. Archived from the original on 4 August 2019. Retrieved 12 October 2017.
  2. Richard A. Singletary (2005). "Bruce Onobrakpeya: His Art and International Reputation". Studies in Urhobo culture. Urhobo Historical Society. p. 632. ISBN 978-067-769-0.